Yadda ganawar tsohon Shugaban kasa Obasanjo da Fulanin Najeriya ta kaya

Yadda ganawar tsohon Shugaban kasa Obasanjo da Fulanin Najeriya ta kaya

A Ranar Asabar, 3 ga Watan Agusta, 2019, tsohon shugaban kasar Najeriya watau Cif Olusegun Obasanjo ya yi wani zama da wasu daga cikin manyan kabilar Fulani da ke Kudancin Najeriya.

Mun samu labarin yadda wannan tattaunawa ta kaya kamar yadda jaridun Najeriya su ka rahoto. Mun tsakuro manyan kanu na wannan zama da a ka yi a Garin Abeokuta da ke cikin jihar Ogun.

Obasanjo da wadannan shugabannin Fulani da ke Kudu maso Yammacin Najeriya da kuma jihohin Kogi da Kwara sun ci ma matsaya. Kadan daga cikin matsayar da aka samu su ne:

1. Wadanda su ka halarci taron sun tabbatar da cewa babu shakka akwai matsalolin rashin tsaro yanzu a Najeriya.

2. Ya kamata a zauna da juna domin ganin yadda za a kawo matsalolin da ke adabbar kasar nan a yanzu.

3. Daga cikin cikas din da a ke samu shi ne kokarin boye gaskiya da yin rufa-rufa a kan abubuwan da ke faruwa.

4. Kyamatar Fulani da a ke yi babbar matsala ce a kasar nan a dalilin bakin jini da wasu bata-gari su ka jawowa sauran Fulani.

5. Akwai Fulani a sauran kasashen Afrika irin su Sanagal, Mali, Nijar, da Guinea inda a ke fama da wadannan matsaloli.

6. Jami’an tsaro su na sakaci wani lokaci wajen maganin matsalolin da a ke samu a lokacin da ya dace.

7. Babu kabilar da ta bazu sosai a kaf Afrika irin Fulani kuma su ma, su na cikin wadanda a ke sacewa a na garkuwa da su a yau.

KU KARANTA: Obasanjo ya na ganawa da wasu shugabannin Fulani a Ogun

A taron an ci ma yarjejeniyar cewa:

8. Dole al’umma su hada kai musamman tsakanin Yarbawa da Fulani wajen ganin an samu sauki.

9. Akwai Fulani da bare cikin masu tada kafar-baya don haka dole a canza salon hukunta Fulani.

10. Dole a tasa shugabannin da ba su yin abin da ya dace a gaba. Ya kamata kuma a rike fallasa masu laifi.

11. A na bukatar hadin kai tsakanin kowa da kowa inda za a rika mika masu laifi a hannun jami’an tsaro.

12. Akwai Fulani da a ka haifa tun fi azal a kasar Yarbawa wadanda Kudancin Najeriya ya zama gidan su don haka babu maganar a fatattake su.

13. Ya kamata majalisu da gwamnatocin jihohin Kudancin Najeriya su shawo kan matsalar kiwon dabbobi.

14. Ya kamata a bankado Makiyan Fulani da ke ta’adi da kuma wadanda ke barna da daga cikin sauran Kabilu domin a hukunta su.

15. Za a sake zama nan da watanni uku domin ganin an dabbaka matakan da a ka dauka a taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel