Iran Ta Amince da Bukatar Amurka, Ta Canza Shawara kan Batun Kera Makamin Nukiliya
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa kasar musulunci ta Iran amince ba za ta kera makamin nukiliya ba
- Wannan kalamai na Trump na zuwa ne bayan tattaunawa ta farko da aka yi tsakanin Amurka da Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan
- Trump ya sanar da cewa da yiwuwar wakilan kasashen za su sake koma teburin tattaunawa a Islamabad a karshen makon nan don cimma matsaya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Iran ta sauya matsayarta kan batun kera makamin nukiliya.
Shugaban Amurka, ya bayyana cewa Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba a cikin yarjejeniyar da ake kokarin kulla wa tsakanin bangarorin biyu.

Source: Getty Images
Amurka da Iran sun fara fahimtar juna

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya yi maganar lokacin kawo karshen yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Ya ce yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai na iya wuce shekaru 20, inda ya bayyana cewa akwai kyakkyawan fata na cimma matsaya nan da 'dan lokaci, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta rahoto.
Trump ya kara da cewa al’amura na tafiya yadda ya kamata, yana mai cewa yiwuwar cimma yarjejeniya da Iran “na da kyau sosai.”
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa ana iya gudanar da wata sabuwar ganawa da tawagar Iran a karshen mako domin ci gaba da tattaunawar.
Da yiwuwar Amurka ta yi sulhu da Iran
Duk da wannan ikirari, rahotanni sun nuna cewa ba a tabbatar da cikakken yarjejeniya ba tukuna, kuma Iran a baya ta musanta wasu ikirarin da ke cewa ta riga ta amince da wasu sharudda.
Sai dai dun da haka, ana ganin cewa kalaman Trump na iya zama wani bangare na kokarin nuna cewa ana samun ci gaba a tattaunawar, duk da cewa har yanzu akwai manyan sabani tsakanin bangarorin biyu.
Mataayar Iran kan kera makamin nukiliya
Batun hana Iran mallakar makamin nukiliya shi ne muhimmin batu a wannan tattaunawa, inda Amurka ke dagewa cewa ba za ta amince da kowace yarjejeniya da za ta bai wa Iran damar mallakar irin wannan makami ba.
Kasar Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kawai, ba domin kera makami ba, kamar yadda tashar NBC News ta ruwaito.

Source: Getty Images
Sai dai da wannan kalamai na Shugaba Trump, za a iya cewa kasashen za su cimma matsaya, wacce aje fatan ta zama sanadiyyar samun zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta yi ikirarin nakasa Khamenei
A wani labarin na daban, kun ji cewa Amurka ta kuma ikirarin cewa jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka a hare-haren da ta kai masa a Tehran.
Wannan ikirari da Amurka ta sake yi na zuwa ne bayan kasashen biyu sun amince da tsagaita wuta na tsawon makonni biyu, kuma sun fara tattaunawar sulhu don kawo karshen yakin gaba daya.
A cewar ministan tsaron Amurka, Peter Hegseth, Mojtaba Khamenei, wanda ya gaji mahaifinsa Ali Khamenei a watan Maris na shekarar 2026, yana raye, amma ya jikkata sosai, har ma ana zargin ya samu nakasa.
Asali: Legit.ng
