Gwamnatin Buhari ta lalata Najeriya - Atiku
Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a yayin babban zabe da aka gudanar a watan Fabraitun 2019, Atiku Abubakar, a ranar Asabar ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta riga ta gama yiwa Najeriya duk wata lalata.
A wata sanarwa da ta fito daga harshen mai magana da yawunsa, Paul Ibe, Atiku ya ce 'yan Najeriya a tsawon shekaru hudu da suka gabata sun yi rayuwa cikin mafi kololuwar kangi na talauci.
Ya ce majalisar dinkin Duniya ta ankarar da 'yan Najeriya dangane da yadda gwamnatin Buhari ta gaza inganta tattalin arzikin kasar nan wanda hakan ya jefa fiye da mutanen kasar miliyan 98 cikin matsanancin katutu na talauci ta kowace siga.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana mamaki kwarai da aniya dangane yadda shugaba Buhari tare da 'yan kanzaginsa suka gaza cewa komai a bisa kididdigar alkalumman talauci da majalisar dinkin Duniya ta fitar game da Najeriya.
Wazirin na Adamawa ya hikaito yadda mafi akasarin al'ummar Najeriya suka juya baya ga Buhari a yayin babban zaben kasa a sakamakon halin kaka-nika-yi na kuncin rayuwa da gwamnatinsa ta jefa su ciki tsawon shekaru hudu da ya shafe a kan gado na mulki.
KARANTA KUMA: Mu daina zargin kowa a kan annobar rashin tsaro a Najeriya - Obasanjo
Ya kara da cewa, rashin daukar dangana da rashi na rungumar kaddara ya sanya Buhari ya yi murdiya ta hanyar magudi, tayar da rikici da tsoratarwa da suka mamaye zaben domin tabbatar da nasarar sa ko ta halin kaka.
A halin yanzu dai babbar jam'iyyar hamayya ta PDP tare da dan takarar ta Atiku, na ci gaba da watsi da zaben shugaban kasa inda tuni ta kalubalanci sakamakon zaben da ta ce an yi magudi a kotun sauraron karar zabe.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng