Jamhuriyyar Nijar ta cika shekara 59 da samun 'yancin kai
A ranar Asabar da ta gabata ne, 3 ga watan Agustan 2019, kasar Nijar ta yi bikin cika shekaru 59 da samun 'yancin kai daga hannun kasar Faransa wadda ta yi maya mulkin mallaka.
Kamar yadda jaridar RFI Hausa ta ruwaito, bikin a wannan karo na zuwa ne daidai da lokacin da matsalolin tsaro suka dabaibaye kasar musamman hare-haren kungiyoyin ta'dda.
Duba da kasancewarta al'ada da aka saba a kocewa shekara yayin bikin murnar samun 'yanci, shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou, a ranar Juma'a da ta kasance jajiberin ranar murna, ya gabatar da jawabai game da halin da kasar ta ke ciki.
Shugaban kasa Issofou yayin gabatar da jawaban sa ya yaba da nasarorin da gwamnatin sa ta samu wajen yaki da ta'addanci da ya alakanta nasarar da taimakon dakarun sojin kasashen ketare da kasar ta samu
Ya kuma yaba da kokarin dakarun Barkhane baya ga sojin kasar Amurka wadanda suka yi tsayuwar daka matuka wajen kakkabe duk wasu miyagun ababe na ta'addanci a fadin kasar.
KARANTA KUMA: Tsare Sowore: Gwamnatin Buhari tamkar ta Abacha ce - Soyinka
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Nijar a yayin wannan rana ta 3 ga watan Agustan kowace shekara, gwamnatin kasar kan iya amfani da wannan dama ta yin dashen itatuwa domin magance matsalar kwararowar hamada.
Tarihi ya tabbatar da cewa, jamhuriyyar Nijar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960 daga hannun kasar Faransa wadda ta yi mata mulkin mallaka. Sai dai masu sharhi sun ce kawowa yanzu kasar na ciki sahun kasashen da talauci ya fi yi wa katutu a nahiyyar Afirka.
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng