Har ila yau: Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin AI duk da haramta zanga-zanga a Abuja

Har ila yau: Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin AI duk da haramta zanga-zanga a Abuja

Duk da haramta zanga-zanga a cikin fadin birnin tarayya, Abuja, da rundunar 'yan sanda ta yi, masu zanga-zanga sun mamaye ofishin kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa (AI), a rana ta uku.

A ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, ne rundunar 'yan sanda ta sanar da dokar hana duk wata zanga-zanga a cikin Abuja domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'umma. An saka dokar ne biyo bayan gumurzun da aka sha tsakanin jami'an rundunar 'yan sanda da mabiya mazhabar Shi'a.

Amma tun ranar Juma'a wasu gungun masu zanga-zanga - da ake kyautatata zaton gwamnati ce ke daukar nauyinsu - sun cigaba da mamaye ofishin AI tare da yin kira ga kungiyar da ta fice daga Najeriya cikin gagga wa.

Masu zanga-zangar na rera wakoki daban-daban, tare da zargin kungiyar AI da yi wa jam'iyyar adawa aiki da kuma goyon bayan makiya Najeriya.

DUBA WANNAN: Hana biza saboda magudin zabe: Amurka ta wanke gwamnatin Buhari, ta yi karin haske

A nata bangaren, kungiyar AI ta ce tun shekarar 1967 ta ke aiki a Najeriya tare da bayyana cewa ba ta da alaka da wata kungiyar siyasa, addini ko kasuwanci. Ta kara da cewa zata cigaba da matsa wa gwamnati lamba a kan ta kasance mai biyayya ga hakkin bil'adama.

Wani bincike da manema labarai suka gudanar ya gano cewa yawancin masu zanga-zangar an debo su ne daga sansanin 'yan gudun hijirav da ke wajen Abuja, kuma da yawansu basu san ma'ana ko aikin kungiyar AI ba da aka tambaye su.

Gwamnatin Najeriya ta zargi AI da goyon bayan duk wani yunkuri na kifar da ita, amma kungiyar ta kafe a kan cewa ta na fafutukar kare hakkin bil'adama ne kawai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel