Latest
Masarautar jihar Kano tace har yanzu bata samu wasika daga gwamnatin jihar Kano ba ta nadin Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.
Hukumar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke shaharraren saurayi mai garkuwa da mutane. Aliyu Sani mai shekaru 20 a duniya mazaunin sabuwar- Unguwa quarters, ya gallabi jihar da satar mutane.
A jiya ne aka cafke wata mata da yara daban-daban har takwas a titin Iwo da ke Ibadan, jihar Oyo. Yaran sun bayyana a jigace ne, dalilin da yasa mutane suka taru tare da tambayar matar. Ta yi ikirarin cewa tana kan hanyar zuwa...
Sanna Marin mai shekaru 34 ta kafa tarihin zama firaiministar Finland mafi kananan shekaru bayan da ta yi nasara a zaben ranar Lahadi. firaiminista Antti Rinne ya yi murabus ne a ranar Talata 3 ga watan Disamba bayan kasa shawo...
Wani saurayi mai shekaru 22 a duniya ya yi garkuwa da kanwarsa a Unguwar Makera da ke karamar hukumar Futua ta jihar Katsina. Hukumar ‘yan sandan jihar kuwa sun cafke saurayin da ya yi wannan aika-aikar.
Masu gabatar da kara sun zargi Felicia da kone bangaren gidan da take ciki domin karkatar da hankalin jama'a zuwa tunanin cewa gobara ce ta tashi a gaba daya, ta kone bangaren gidajen nasu. A cikin takardar karar, gwamnatin jihar
Gwamnatocin Najeriya da kasar Iran sun fara tattaunawa na musamman kan shugaban kungiyar mabiyar addinin Shi'an Najeirya, Ibrahim el-Zakzaky.
Wani Hadimin Sanata O. Omo Agege, E. Ugbarugba ya sha da kyar bayan an yi yunkurin kashe shi a Delta. An harbi Mai ba babban Sanatan na APC shawara ne cikin dare kamar yadda ya shaidawa Manema labarai.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Muhammad M Nami a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS, biyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Mista Babatunde Fowler.
Masu zafi
Samu kari