Nayi garkuwa da kanwata ne don samun kudin hidimtawa budurwata - Wanda ake zargi

Nayi garkuwa da kanwata ne don samun kudin hidimtawa budurwata - Wanda ake zargi

Wani saurayi mai shekaru 22 a duniya ya yi garkuwa da kanwarsa a Unguwar Makera da ke karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina. Hukumar ‘yan sandan jihar kuwa sun cafke saurayin da ya yi wannan aika-aikar.

An gano cewa, Ibraheem Kazeem ya hada baki ne da budurwarsa mai suna Murja don garkuwa da kanwarsa mai suna Asiay Kazeem. Sun cafke Asiya ne a yayin da take dawowa daga Islamiyya a ranar 16 ga watan Afirilu 2019.

Budurwar ta shi ce ta kula da karamar yarinyar da suka kai karamar hukumar Talata Mafara da ke jihar Zamfara. Duk da an bukaci kudin fansa har naira miliyan uku, amma Ibraheem ya roki kungiyar masu garkuwa da mutanen da su amince da naira dubu dari biyun da mahaifinsa ya amince zai iya biya. Hakan ya biyo bayan tsoratar da Ibraheem ya yi ne.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Reinhard Bonnke

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da cafke wanda ake zargin kuma ya bayyana cewa, an mika lamarin ga sashin binciken laifuka na musamman na hukumar ‘yan sandan jihar.

Kamar yadda Ibraheem ya sanar da manema labarai, ya ce: “Budurwata ta kawo min ziyara kuma na ajiyeta a dakina da yake wajen gidanmu. Babu wanda ya san tazo. Amma kuma banda kudin da zan bata. Sai ta bani shawarar mu yi garkuwa da kanwata don samun kudin da zan bata. Ta tabbatar min da cewa, mahaifinmu ba zai yi kasa a guiwa ba wajen biyan kudin fansa,”

Ya kara da cewa, “A ranar da take dawowa daga Islamiyya, na kaita wajen budurwata wacce take kan babur. Da kaina na dinga rokonsu da su sako ta saboda tashin hankalin da batan Asiya ya jawo. A halin yanzu na kunyata kaina”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel