Bidiyon Jessica Cox: Direbar jirgin sama ta farko a duniya da take tukin jirgi da kafa

Bidiyon Jessica Cox: Direbar jirgin sama ta farko a duniya da take tukin jirgi da kafa

- Jessica Cox, wacce ta kammala digirinta daga jami’ar Arizona, ta kafa tarihin zama matukiyar jirgi ta farko amma mara hannu

- An haifeta da wannan nakasar ne kuma tana amfani da kafarta ne wajen yin aiyuka da yawa kuma ta samu nasarar karbar bakar damara a taekwondo

- Jessica ta taba shiga gasar gudu ta mil 40 da El Tour de Tuscon suka shirya kuma ta rubuta littafi mai suna ‘Disarm Your Limits’

Nakasa ba tawaya bace a rayuwa. Labarin Jessica Cox na daya daga cikin labaran da suka tabbatar da hakan. Duk da cewa an haifeta babu hannaye, bata taba barin hakan yasa ta yi nakasasshiyar rayuwa ba.

Ta samu nasarar karbar bakaradamara a gasar taekwaondo, kuma tana sauran al’amuran rayuwarta kamar yadda masu hannaye ke yi. Tana kida da Piano da wasu abubuwan kida. Daga cikin manyan ababen al’ajabi da hazakar Jessica sune, zamanta matukiyar jirgi ta farko a duniya mara hannu.

Jessica tace, mutane da yawa na kallon rashin hannunta a matsayin nakasa, amma tana son musanta zarginsu.

Mijinta da yace zai kwatanta ta da kalmomi uku, zasu zama “saukin kai, kokari kuma jarumta”, Jessica ta fara kokarin zama matukiyar jirgin sama ce bayan da wani matukin jirgin sama na yaki, ya tunkareta da batun ko zata so zama irinshi.

KU KARANTA: Lamari ya canja mai shari'a ta shiga hannu: An kama alkali tana iskanci da lauyoyinta guda uku a cikin kotu

Jessica ta samu lasisinta ne ranar 10 ga watan Oktoba 2018, bayan da ta samu horarwa ta shekaru uku kuma aka tabbatar da zata iya tuka jirgin sama.

Jarumtarta a kan kwatanta ta da zuciyar maza bayan da ta kammala gudun mil 40 na El Tour de Tuscon kuma ta wallafa littafin kanta mai suna ‘Disarm Your Limits’. Littafin ya kunshi tarihin rayuwarta da abubuwan da suka bata kwarin guiwa.

Ya kamata mai karatu ya san cewa, ta kammala digirinta ne a jami’ar Arizona a shekarar 2005 a bangaren nazarin halayyar dan Adam.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel