Kisan kishiya da 'ya'yanta 7: Kotu ta yanke wa matar aure hukuncin kisa

Kisan kishiya da 'ya'yanta 7: Kotu ta yanke wa matar aure hukuncin kisa

Wata kotun jihar Ebonyi da ke zamanta a Abakaliki ta yanke wa wata mata, Agnes Nwefuru, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe kishiyarta da 'ya'yanta guda bakwai.

A takardar kara mai lamba HAW/13C/2017, gwamnatin jihar Ebonyi ta gurfanar da Felicia Nwefuru bisa zarginta da laifin saka wuta a gidan kishiyarta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta da 'ya'yanta bakwai.

Masu gabatar da kara sun zargi Felicia da kone bangaren gidan da take ciki domin karkatar da hankalin jama'a zuwa tunanin cewa gobara ce ta tashi a gaba daya, ta kone bangaren gidajen nasu.

A cikin takardar karar, gwamnatin jihar ta zargi Felicia da kwashe kayanta da na 'ya'yanta daga cikin gidan da take kafin daga bisani ta saka wuta a gidan.

Felicia ta aikata laifin ne a cikin shekarar 2017 da misalin karfe 3:00 na dare a garin Ogboji da ke yankin karamar hukumar Ishielu a jihar Ebonyi.

Mutane biyu ne kacal suka tsira bayan Felicia ta saka wuta a gidan, mutane sune mijin Felicia, Mista Sylvanus Nwefuru, da kuma wata diyarta mai suna Ukamaka.

Wutar gobarar ta lashe rukuni biyu a cikin gidan mijinsu Felicia.

Da yake yanke hukunci a kan karar, alkalin kotun, Jastis Uwabunkonye Onwosi, ya bayyana cewa masu kara sun tabbatar da cewa Felicia ta aikata laifin da ake zarginta da shi, a saboda haka kotu ta yanke mata hukunci ta hanyar rataya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel