Jerin sunayen 'yan majalisar Sarkin Karaye da ya rantsar

Jerin sunayen 'yan majalisar Sarkin Karaye da ya rantsar

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II a ranar Litinin ya rantsar da kwamitin majalisar masarautarsa kuma sun yi taron farko a fadar Sarkina. Rantsarwar ta samu halarta shuwagabannin kananan hukumomi da kuma wasu manyan masu sarauta a masarautar ta Karaye.

Wannan na kunshe ne a takardar da jami’in yada labarai na masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ya fitar tare da mikata ga jaridar solacebase a ranar Litinin.

Idan zamu tuna dai, Gwamna Ganduje na jihar Kano ya samu nasarar tabbatar da dokar karin masarautu hudu a jihar bayan da majalisar jihar ta amince a ranar Alhamis.

Takardar tace, Sarkin Karaye wanda shine shugaban majalisar masarautarsa, ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ya sa hannu a kan dokar kirkirar sabbin masarautun a jihar.

DUBA WANNAN: FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

Basaraken, kamar yadda takardar ta sanar, ya jinjinawa gwamnatin jihar da majalisar jihar a kan abinda ya kwatanta da babban kokari wajen tabbatar da sun cika bukatar mutanen jihar.

A taron, wanda aka tattauna lamurran tsaron masarautar, an bukaci hakimai da dagatai da su samarwa masu unguwanni rijistar da zasu dinga daukar sunan duk wani bako da ya shigo yankin masarautar.

A matsayin hanyar tabbatar da zaman lafiya, tsaro da lumana a yankin masarautar, majalisar ta jaddada cewa akwai bukatar ‘yan kasuwa, shuwagabanni addinai da sauran masu ruwa da tsaki a yankin da su saka hannu wajen tabbatar da tsaron masarautar da jihar baki daya,” in ji takardar.

Taron ya amince da Alhaji Tijjani Usman Getso a matsayin sakatare masarautar. Sauran mambobin majalisar masarautar karayen sun hada da: Alhaji Isma’ila Gwarzo, Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa, Alhaji Lawan Sule Garo, Barista Balarabe Bello Rogo, Alhaji Sidi Mustapha Karaye da Alhaji Wada Na Kofar Yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel