An fara tattauna tsakanin Najeriya da Iran kan lamarin El-Zakzaky

An fara tattauna tsakanin Najeriya da Iran kan lamarin El-Zakzaky

Gwamnatocin Najeriya da kasar Iran sun fara tattaunawa na musamman kan shugaban kungiyar mabiyar addinin Shi'an Najeirya, Ibrahim el-Zakzaky.

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Seyed Abbas Mousavi, a ranar Lahadi ya bayyana cewa ana yarjejeniya da jami'an Najeriya kan yadda za'a inganta rayuwar El-Zakzaky da ya kasance a tsare tsawon shekaru hudu yanzu.

Ya ce mataimakin shugaban kasan kan tattalin arziki, Mohammed Nahawandian, ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a Malabo, kasar Equatorial Guinea, kan lamarin El-Zakzaky.

Ya ce sun gana ne lokacin da suka halarci taron kasashe masu fitar da iskar gas GEC a Equatorial Guinea.

Mousavi yace: "Bangarorin biyu sun tattauna kan hadin kan tattalin arziki, diflomasiyya da kuma lamarin El=Zakzaky."

"Gwamnatin kasar Iran a ganawar da tayi da takwararta Najeriya a Tehran da Abuja, ta tattauna yadda za'a inganta rayuwar Zakzaky a kurkuku."

Babbar kotun tarayya dake zaune a Kaduna ta bada umurnin dauke shugaban kungiyar mabiyar akidar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, daga ofishin hukumar DSS.

Alkalin ya bayyana cewa a mayar da Sheikh Zazzaky gidan gyara halin jihar Kaduna.

Alkaliy mai shari'a, Jastis Gideon Kudafa, ya bayyana cewa dalilin da yasa a bada wannan umurni shine domin baiwa likitoci da lauyoyin El-Zakzaky daman ganinshi lokacin da suke bukata.

Saboda haka, ya dage karan zuwa ranar 6 ga watan Febrairu, 2019 don cigaba da sauraron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel