Garba Shehu ya mika 'kambun' gwarzon shekara ga Dino Melaye

Garba Shehu ya mika 'kambun' gwarzon shekara ga Dino Melaye

Sanannen dan siyasar Najeriya kuma Sanata a majalisar dattawan kasar nan har sau biyu, Dino Melaye, an karramashi da kyautar ‘Gwarzon shekara' a ranar Lahadi. Wata jaridar yanar gizo mai suna ‘Kwararafa Reporters' ce ta karrama tsohon sanatan, kwanaki kadan baya da ya sha kaye a zaben komawa majalisar.

Kamar yadda jaridar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, an karramashi ne don karfafa ‘yan Najeriya da su rungumi shugabanci nagari da kuma duban bukatar mutane ta zamo kan gaba a mulkinsu. Hakan kuwa zai tabbata ne ta hanyar jajircewa, aiki tukuru, nagarta da kuma shugabanci nagari irin wanda Melaye ya bayyana da sauran masu karbar lambar yabon.

Wadanda suka samu halartar wajen taron karramawar sun hada da hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu.

Amma kuma, anyi karamin wasan kwaikwayo bayan da mashiryan bada lambar yabon suka bukaci Garba Shehu da ya mika lambar yabon ga tsohon Sanatan Najeriyan.

Kiran sunan Garba Shehu kuwa yasa mutanen wajen suka fara tafi da sowa cike da mamaki.

DUBA WANNAN: FIRS: Fowler ya gode wa Buhari, ya 'sace' gwuiwar masu cewa an cire shi

Hatta Melaye da ke tsaye yayin da aka kira sunan wanda zai mika masa lambar yabon, bai iya jurewa ba sai da ya kyalkyale da dariya.

Garba Shehu kuwa ya taso don mika lambar yabo ga Melaye, lamarin da ya kara sa dariya da shewa daga masu kallo.

Cike da barkwanci bayan ya karba lambar yabon, Garba Shehu ke tambayar ‘yan kallo: “Ko dai in tafi da wannan lambar yabon ne in barshi a tsaye?”

Ya sanar da bakin cewa, yana da kusanci da Melaye duk da ba jam’iyyar siyasarsu daya ba. Ya kara da cewa, akwai aiyuka masu yawa da suka yi tare da tsohon sanatan. Ya bayyana yadda siyasa ke iya hada mutane kuma ta rabasu.

A mayar da martanin da Dino Melaye ya yi bayan karbar lambar yabon, ya kwatanta Garba da aboki kuma dan’uwa. Ya tabbatar da cewa, dangantakarsu ta yi dadewar fiye da abunda ya faru cikin kwanakin nan.

“A yayin da nake mika godiyata gareshi, ina kuma mika godiyata ga mashiryan bada wannan lambar yabon,” Melaye yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel