Tashin hankali: An kama tsohuwa da yara kanana guda takwas za ta sayar da su

Tashin hankali: An kama tsohuwa da yara kanana guda takwas za ta sayar da su

- A jiya ne aka cafke wata mata da yara daban-daban har su takwas a titin Iwo dake Ibadan, jihar Oyo

- A yadda mutane suka lura da yaran a gajiye tare da duban yanayin matar, yasa suka tsareta da tambaya

- Matar ta kasa amsa tambayoyin amma tayi ikirarin cewa majami’a zasu je da kananan yaran

A jiya ne aka cafke wata mata da yara daban-daban har takwas a titin Iwo da ke Ibadan, jihar Oyo. Yaran sun bayyana a jigace ne, dalilin da yasa mutane suka taru tare da tambayar matar. Ta yi ikirarin cewa tana kan hanyar zuwa majami’a ne da yaran.

Bayan taruwar mutanen tare da tambayoyin da ta amsa, sun gano cewa babu kamshin gaskiya a lamarin matar.

A bidiyon, matar ta bayyana a tsorace kuma babu kwarin guiwa. Hakan yasa ta kasa magana ko bayyana wa mutanen da suka yi dafifi a kanta, inda ta nufa da kananan yaran.

Ba dai a yanzu aka fara satar yara a kasar nan ba. Wasu yaran a kan daukosu ne daga yankinsu a kaisu wani yanki daban na kasar nan inda ake siyar dasu.

KU KARANTA: Tirka-tirka: Miji ya nemi matarshi ta kawo mishi buhun shinkafa 30, shanaye 6 da N52,000 kafin ya sake ta

A kwanakin bayan ne aka samu gano wasu yara 9 da aka sace daga jihar Kano ta arewacin Najeriya, amma aka siyar dasu a kudancin kasar nan. Yaran da aka siyar din a jihar Anambra, sun bar gida ne tun da kankantarsu. Dalilin da yasa suka dawo gida basu jin yaren hausa kwata-kwata.

Bayan sacesun da siyar dasu, an canza musu addinansu. Daga addinin musulunci sun koma addinin kirista kuma an basu sunayen kabilar Igbo.

Daga wannan lokacin ne aka cigaba da bankado kananan yaran da aka sace, aka siyar dasu a wani yanki na kasar nan. Jami’an tsaro bas u yi kasa a guiwa ba wajen cafko wadanda ke safarar yaran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel