Lamari ya canja mai shari'a ta shiga hannu: An kama alkali tana iskanci da lauyoyinta guda uku a cikin kotu

Lamari ya canja mai shari'a ta shiga hannu: An kama alkali tana iskanci da lauyoyinta guda uku a cikin kotu

- An kama wata alkalin Kentucky mai suna Dawn Gentry da laifuka har guda tara

- Laifukan sun hada da lalata da maza biyu a lokaci daya a dakin kotu da fifita lauyoyin da suka kwanta da ita

- An kama ta da laifin daukar ma’aikatan kotun ba bisa ka’ida ba sai bisa iya kwanciya da ita

Wata alkalin Kentucky an kama ta da laifukan rashin da’a har guda tara bayan da sannan an kama ta da laifin kwanciya da maza biyu a lokaci daya a cikin dakin kotu.

Dawn Gentry mai shekaru 38, an zargeta ne da amfani da kujerarta don tirsasa lauyoyin wajen aikata wannan shagala.

Alkalin kotun asalin ‘yar yankin Kenton County ce a Kentucky, kuma ta kai wannan babban matsayin ne a watan Nuwamba 2018. An zargi cewa takan shayar da wadanda take dauka aiki da barasa, itama ta sha sannan ta kuma tana kwanciya da maza biyu a lokaci daya. Alkalin ta kan fifita lauyoyin da suka kwanta da ita ko a yayin shari’a.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama tsohuwa da yara kanana guda takwas za ta sayar da su

Jaridar Cincinnati Enquirer ta ruwaito cewa, lauya Katherine Schulz ta datse dangantakarsu bayan da ya zargi Gentry da neman mijinta da lalata ta kafar sada zumunta. Alkalin ta kara da bukatar lauyar da ta ja hankalin tsohon mijinta ta yadda zata gurfanar dashi a kan laifin cin amana.

Duk da wakilan Gentry sun musanta aukuwar lamarin. Amma daga bisani an kama Gentry da laifuka masu tarin yawa da suka hada da: Lalata da maza biyu a lokaci daya a dakin kotun, daukar aiyuka ba bisa ka’ida ba, fifita lauyoyi mazan da suka kwanta da ita da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel