Hatsabibin mai garkuwa da mutane da ya gallabi jihar Katsina, ya shiga hannu

Hatsabibin mai garkuwa da mutane da ya gallabi jihar Katsina, ya shiga hannu

Hukumar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke shaharraren saurayi mai garkuwa da mutane. Aliyu Sani mai shekaru 20 a duniya mazaunin Sabuwar- Unguwa kwatas, ya gallabi jihar da satar mutane.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin a jihar Katsina. Yace an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 4 ga watan Disamba bayan samamen da suka kai.

"A watan Afirilu, wanda ake zargin ya hada kai da wani Abdulrahman Danfillo mai shekaru 25, inda suka yaudara tare da garkuwa da Abubakar Muhammad da Aliyu Ahmed, duk a Sabuwar-Unguwa a Katsina." inji SP Gambo.

DUBA WANNAN: 2023: Wata kungiyar Arewa ta mara wa Tinubu baya

"Wadanda ake zargin sun kai wadanda suka sace wajen wasu 'yan daba a dajin Gora, dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina don garkuwa dasu. Mahaifin Abubakar Muhammad ya biya dubu dari da hamsin kafin a sakeshi, amma Aliyu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen," in ji shi.

Yace, ana cigaba da bincike don kamo sauran 'yan kungiyar. Isah ya kara da cewa, 'yan sandan sun cafko wasu mutane uku da suke tura sakon barazana don firgita wani Shu'aibu Bala mai shekaru 36 da ke Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar.

Yace wadanda ake zargin, suna barazanar sace Bala ne ko wani a iyalansa inda suka karbar mishi naira dubu dari da hamsin. Kamar yadda ya sanar, rundunar 'yan sanda ta Operation Puff Adder, wacce DPO Kafur ya jagoranta, ta yi nasarar cafke wasu 'yan kungiyar dake Unguwar Illiya. Sun cafkesu ne a yayin da suka je karbar kudin fansan da suka bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel