Kotu ta yanke wa matar da ta kashe kishiyarta da 'ya'yan ta 7 hukuncin kisa

Kotu ta yanke wa matar da ta kashe kishiyarta da 'ya'yan ta 7 hukuncin kisa

Babban kotun jihar Ebonyi da ke zamanta a Abakaliki, babban birnin jihar a ranar Litinin ta yanke wa wata mata, Misis Agnes Nweferu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe kishiyarta da 'ya'yanta bakwai.

Gwamnatin jihar ta shigar da karar Nweferu ne a kotun inda ake zargin ta da bankawa kishiyarta, Felicia Nweferu da 'ya'yanta bakwai wuta wadda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsu.

A cewar 'yan sandan, wanda ake zargin ta kuma kona gidanta yayin aikata mummunan aikin domin kawar da hankalin al'umma kan abinda ta aikata.

Masu shigar da kara sun kuma bayyana cewa wace aka yi karar ta kwashe dukkan kayan ta da na 'ya'yan ta zuwa wani wuri a waje kafin ta bankawa gidan wuta.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta yi wa minister kaca-kaca, ta bukaci a rika hukunta masu zagin shugaban kasa

A 2017, mutane takwas 'yan gida daya sun kone kurmus sakamakon wani gobara mai ban mamaki misalin karfe 3 na dare a garin Ogboji a karamar hukumar Ishielu na jihar Ebonyi.

Mutane biyu ne suka tsira daga gobarar, mai gidan, Mista Sylvanus Nweferu da Miss Ukamaka Nweferu daya daga cikin 'ya'yan mai gidan.

Gobarar ta lashe dakuna biyu a cikin gidan.

Yayin zartar da hukuncin, alkalin kotun Mai shari'a Uwabunkonye Onwosi, ya bayyana cewa kotu ta samu wanda aka yi kara da aikata laifin da ake tuhumarta da shi.

A cewar alkalin, "An samu Nweferu Agnes da laifin aikata kisar gilla saboda haka an yanke mata hukunci. Hukuncin ta shine za a rataye ta har sai da mutu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel