Mune muka tsugunna muka haifi Kannywood, kuma sakacin mu ne yasa ta ruguje - Kamaye na Dadin Kowa

Mune muka tsugunna muka haifi Kannywood, kuma sakacin mu ne yasa ta ruguje - Kamaye na Dadin Kowa

- Fitacce kuma tsohon jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Dan Azumi Baba wanda aka fi sani da Kamaye na 'Dadin Kowa' yayi magana akan abin da ya kawo koma baya a masana'antar Kannywood

- Jarumin ya ce sakacin su ne ya janyo masana'antar ta lalace

- Ya ce sune suka tsugunna suka haifi masana'antar kuma da ace tun a lokacin sun dauketa da muhimmanci da yanzu ba a san inda za ta kai ba

Fitaccen jarumin wasan barkwancin nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Dan Azumi Baba Tsamiyar 'Yan Gurasa, wanda aka fi sani da Kamaye, ya bayyana cewa sakacin su ne ya sanya masana'antar Kannywood ta ruguje gabaki daya.

Kamaye ya bayyana hakan a lokacin da yake hira da gidan rediyon Freedom dake jihar Kano, inda ya kara da cewa sune suka samar da masana'antar tun farko, amma saboda rashin kula da sakaci ya sanya yanzu duk ta lalace.

Jarumin ya bayyana cewa kwata-kwata basu dauki sana'ar ta wasan Hausa da wani muhimmanci ba, kuma hakan shine ya jawo koma baya a masana'antar.

Ya ce a lokacin da suka fara kafa masana'antar ba su taba tunanin cewa za ta kai wannan matsayin ba, kuma hakan ne ya sanya basu bata muhimmanci ba a wancan lokacin, sai gashi kuma cikin ikon Allah yanzu masana'antar ta wuce yadda ake tunaninta.

KU KARANTA: Bidiyon Jessica Cox: Direbar jirgin sama ta farko a duniya da take tukin jirgi da kafa

Jarumin dai yana daya daga cikin fitattun jaruman da suke fitowa a cikin shirin nan da ake yi na 'Dadin Kowa'.

Idan ba a manta ba makonnin da suka gabata, abokiyar wasan barkwancin shi, wacce take fitowa a matsayin matar shi a cikin shirin 'Dadin Kowa' tayi maganar cewa yanzu ita a shirye take domin taga ta aure shi a gaske, amma fa idan har shi ya shirya aurenta.

Har ya zuwa yanzu dai jarumin bai ce komai dangane da maganar da matar tayi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng