Sanna Marin: Budurwa ta farko da ta zama Firaiminista tana da shekara 34 a duniya

Sanna Marin: Budurwa ta farko da ta zama Firaiminista tana da shekara 34 a duniya

- Sabuwar zababbiyar Firaiminista Sanna Marin zata kafa tarihin zama firaiminista mafi karancin shekaru a duniya

- Zata hau mulkin kasar Finland tana da shekaru 32 kacal a duniya bayan da Antti Rinne ya yi murabus

- Ta bayyana cewa, karancin shekaru ko jinsi bai taba zama abinda take duba a siyasa ba

Sanna Marin mai shekaru 34 ta kafa tarihin zama firaiministar Finland mafi kananan shekaru bayan da ta yi nasara a zaben ranar Lahadi. firaiminista Antti Rinne ya yi murabus ne a ranar Talata 3 ga watan Disamba bayan kasa shawo kan wani yajin aiki da ya yi.

Tsohuwar ministar sufurin wacce jam'iyyarta ce mafi girma, zata kasance firaiminista mafi karancin shekaru a duniya idan aka rantsar da ita a kwanaki kadan masu zuwa.

"Muna da aiyukan da ke jiranmu don kara samun yardar mutane," Marin ta sanar da manema labarai bayan da samu nasarar zabe.

"Ban taba kallon karancin shekaru na ko jinsi na ba. Nakan tuna dalilina na shiga siyasa da kuma abinda yasa masu zabe suka amince min."

Jam'iyyun siyasa hudu na kasar Finland ke karkashin shugabancin mata. Jam'iyyar Left Alliance wacce Li Anderson mai shekaru 32 ke jagoranta, Jam'iyyar Green League wacce Maria Ohisalo mai shekaru 34 ke jagoranta, jam'iyyar Centre Party wacce Katri Kulmuni mai shekaru 32 ke jagoranta sai kuma Swedish People's Party wacce Anna-Maja Henriksson mai shekaru 55 ke jagoranta.

KU KARANTA: Bamu kama shi ba wannan karon, amma tabbas sai munyi mishi dukan tsiya idan muka kama shi - Cewar wadanda suka kaiwa Amaechi hari

Marin wacce zata kafa babban tarihin, kwararriya ce a siyasar Finland. Ta shiga harkar shugabanci da siyasa ne tun tana da shekaru 27. Zata karbi shugabancin ne ana tsaka da yajin aikin kwanaki uku wanda akwai yuwuwar ya tsayar da al'amuran kamfanonin kasar daga ranar Litinin 9 ga watan Disamba.

Hukumar kula da masana'antun kasar sunyi kiyasin cewa, za a iya asarar euro miliyan 500 a kudin shigar kasar.

Wasu daga cikin shuwagabannin kasashen duniya masu kananan shekaru sun hada da: Jacinda Ardern ta kasar New Zealand mai shekaru 39, firaiministan Ukraine Oleksiy Honcharuk mai shekaru 35 sai kuma shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong-un mai shekaru 35.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel