Har yanzu ba mu shaida naɗin Sanusi ba - Masarautar Kano

Har yanzu ba mu shaida naɗin Sanusi ba - Masarautar Kano

Masarautar jihar Kano tace har yanzu bata samu wasika daga gwamnatin jihar Kano ba ta nadin Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar.

Wata majiya mai karfi wacce take da kusanci da Sarkin, ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa koda suka karanta nadin a kafafen sada zumuntar zamani, masarautar har yanzu bata samu wasika daga gwamnatin jihar ba.

“Tabbas mun karanta labarin a kafafen sada zumuntar zamani da kafofin yada labarai na nadin mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano. Amma, har yanzu gwamnatin jihar bata mika wasikar hakan ga masarautar ba,” cewar majiyar.

“A safiyar Litinin ne muka tashi da wannan labarin nadin, amma har a wannan lokacin da muke magana bamu samu wasika daga gwamnatin jihar ba. Idan muka samu wasikar, zamu yi nazarinta sannan mu mayar da martani. Amma a yanzu, ba zamu iya mayar da martanin komai ba tunda babu abinda ya iso mana,” majiyar ta ce.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta yi wa minister kaca-kaca, ta bukaci a rika hukunta masu zagin shugaban kasa

Majiyar ta sanar da hakan ne a yayin mayar da martani ga labaran da ke yawo a kafafen yada labarai na nadin Sarki Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar Kano.

A takardar da sakataren yada labarai na jihar Kano, Abba Anwar ya fitar, ya bayyana cewa wannan nadin ya yi biyayya ne ga sashi na 4, sakin layi na 2 da kuma sashi na 5, sakin layi na 1 da 2 dake kunshe a dokokin masarautar jihar Kano ta 2019. Wadannan dokokin kuwa sun ba wa gwamnan damar yin wannan nadin.

Wannan nadin ya fara aiki ne daga ranar Litinin, 9 ga watan Disamba 2019, kamar yadda takardar ta sanar.

Sauran ‘yan majalisar sarkin sun hada da manyan sarakunan Bichi, Rano, Karaye da Gaya. Sun hada da Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Dr Tafida Abubakar (Autan Bawo), Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II da Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel