An yi yunkurin kashe wani Hadimin Ovie Omo Agege a Jihar Delta

An yi yunkurin kashe wani Hadimin Ovie Omo Agege a Jihar Delta

Wani daga cikin Hadiman Sanata Ovie Omo-Agege ya tsallake rijiya da baya da baya bayan an harbe shi da bindiga. Har sai da ta kai harsashi ya fasa tagar motar da Hadimin ya ke ciki.

Efe Ugbarugba, ya tsira da ran sa a harin da aka kai masa a Garin in Otokutu-Agbarha da ke cikin karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. Wasu Miyagu ne su ka bude masa wuta.

Mista Ugbarugba, shi ne Mai taimakawa Sanata Ovie Omo-Agege a kan harkokin Matasa a majalisar dattawa. An kai masa wannan hari ne a Ranar Laraba 4 ga Watan Disamba, 2019.

Hadimin Sanatan ya shaidawa Jaridar The Nation cewa wannan abu ya auku ne cikin dare bayan ya sauke Mai dakinsa da ‘Dansa a gida. Da ya ke ya taki sa’a, ba a iya yin nasarar hallaka shi ba.

KU KARANTA: Hadiman Sanata Omo Agege da Wase sun koka da rashin albashi

Mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce an buda masa wuta ne a kan titi yayin da ya tunkari wasu ‘Yan bindiga. A cewarsa ana fara harbinsa, ya yi maza ya taka mota ya tsere.

Wadannan mugaye sun fasa gaban motarsa da harsashi yayin da su ka yi ta harbin shi da bindiga ko ta ina. Ugbarugba ya ke cewa Ubangiji kurum ya tsaga ya na da sauran kwanaki a Duniya.

Bawan Allan ya shaidawa Manema labarai cewa Miyagun sun yi ta sakin masa wuta, har harsashi ya taba kansa bayan bula gaban motarsa. Daga nan ya yi maza ya zura gaban ‘yan sanda.

“Ina kira ga Jami’an tsaron mu su gano wadannan ‘Yan bindiga da su ke neman kashe ni babu wani dalili. Shi yasa na ke kira a kara inganta tsaro a kusa da ni.” Inji Ugbarugba bayan harin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng