Kashe Ministan Taron Mali Ya Rikita Najeriya, Ta Kawo Mafita kan Ta'addanci

Kashe Ministan Taron Mali Ya Rikita Najeriya, Ta Kawo Mafita kan Ta'addanci

  • Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da kashe ministan tsaron Mali, Sadio Camara, bayan harin ta’addanci da ya rutsa da shi a gidansa
  • Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce ta’addanci barazana ce ga yankin Sahel, tana bukatar hadin kai tsakanin kasashe a yankin
  • Gwamnatin tarayya ta jaddada goyon baya ga Mali wajen kare ikon kasarta, tabbatar da tsaro, da samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin yammacin Afirka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi magana bayan kusan ministan tsaron kasar Mali a cikin gidansa.

Gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai da kashe, Sadio Camara wanda ya tayar da hankali musamman a yankin Sahel.

Najeriya ta yi magana kan kashe ministan tsaron Mali
Ministan tsaron kasar Mali, Sadio Camara yayin taro a Bamako. Hoto: FANNY NOARO-KABRE/AFP.
Source: Getty Images

Hakan na cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar a Facebook inda ta ce Camara ya mutu ne bayan samun munanan raunuka sakamakon harin bam da aka kai kusa da gidansa.

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka

Najeriya ta yi jimamin kisan ministan tsaron Mali

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana lamarin a matsayin mummunan sakamakon ta’addanci.

Harin ya kasance cikin wasu hare-hare masu yawa da suka afku a birnin Bamako da sauran garuruwa a Mali.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ‘yan aware sun kai hare-haren hadin gwiwa a wurare daban-daban, har da babban birnin kasar.

An ce mayaƙan Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin, wata kungiyar da ke da alaka da al-Qaeda a yankin Sahel, tare da ‘yan kungiyar Azawad Liberation Front ne suka kai harin hadin gwiwar.

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce rasuwar Camara ta zo ne a wani lokaci mai muhimmanci a tarihin kasar Mali.

Gwamnatin Tinubu ta kadu da aka hallaka ministan tsaron Mali
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da marigayi ministan tsaron Mali, Sadio Camara. Hoto: Bayo Onanuga, FANNY NOARO-KABRE/AFP.
Source: Getty Images

Shawarar da Najeriya ta bayar kan ta'addanci

Sanarwar ta ce hare-haren tashin hankali da ke faruwa a yankin Sahel suna nuna bukatar karin hadin kai tsakanin kasashen yankin da sauran abokan hulda na duniya domin yaki da matsalar tsaro.

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25

“Ta’addanci, a dukkan nau’o’insa da yadda yake bayyana, yana ci gaba da kasancewa abokin gaba na bai daya da ke bukatar hadin kai, ci gaba da hadaka, da sake tabbatar da dan’adamtakarmu ta bai daya.”

Najeriya ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Mali wajen kare ikon kasarta, tabbatar da cikakken yankinta, da dawo da zaman lafiya da tsaro mai dorewa ga al’ummarta.

Gwamnatin tarayya ta kuma bayyana kudirinta na ci gaba da aiki tare da Mali da sauran kasashe ta hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa wajen yaki da matsalar ta’addanci.

“A wannan lokaci na alhini, Najeriya ta sake yin kira da a karfafa hadin kai tsakanin kasashe, karkashin ka’idojin mutunta juna da tsaro na bai daya.”

- Cewar sanarwar

Shugaban Mali ya magantu kan kisan minista

A wani labarin, an ji cewa shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali, Assimi Goita, ya yi magana bayan harin yan ta'adda wanda ya yi ajalin Ministan tsaro, Sadio Camara.

Goita ya tabbabar cewa gwamnati na kokarin kan lamarin bayan hare-haren da suka hallaka jama'a tare da jikkata mutane da dama

Kungiyoyin masu ikirarin jihadi masu alaƙa da Al-Qaeda sun kai hare-hare a sansanonin soji da kusa da filin jirgin Bamako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.