Latest
Mataimakin gwamnan jihar Taraba, Haruna Manu ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon annobar Coronavirus a jihar kuma duk wanda ya kamu da cutar ya warke.
Sani Adamu mai ritaya ya aika bidiyo ga Muhammadu Buhari, ya ce ya yi masa aiki a 1964 a barikin Legas, amma yanzu karfinsa ya kare don haka ya ke neman abinci.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, kaso 51 cikin 100 na duk adadin masu cutar korona a Najeriya sun kasance a wasu kananan hukumomi 9 kacal da ke fadin kasar.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr Doyin Okupe, a ranar Litinin ya bada labarin abinda ya fuskanta yayin da yake cibiyar killacewa don jinyar cutar coronavirus.
Ta ce an kama sojan ne sanye ka kayansa na aiki yana tuki tare da wasu fasinjoji guda uku a cikin mota daga Abuja kuma ba su sanye da takunkumin rufe fuska.
Sai dai a wannan karon, duba da hali na musamman da annobar Coronavirus ta jefa duniya, Asheikh yace ana iya yin sallar ba tare da an gudanar da huduba ba.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa a Masallatan Juma’a za’a gudanar da sallar Idi a bana a jahar Sakkwato da kewaye.
Za ku ji cewa gwamnatin shugaba Buhari ta nada sabon Shugaban Jami’ar da ke Jihar Shugaban kasa. Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ne ya zama Shugaban Jami’ar FUDMA
Gwajin da aka gudanar a kan mutane 45 bayan shan maganin da suke kiran shi da suna, mRNA-1273, ya nuna cewa jikinsu ya samu riga-kafin kwayar cutar korona.
Masu zafi
Samu kari