Buhari: Na taba yi maka aiki a bariki, ka taimaka mani - Sani Adamu, mai ritaya
A wani gajeren bidiyo na kusan mintuna biyu da rabi da Mustafa Bulama ya wallafa a shafinsa na Tuwita, an ga wani tsohon soja ya na rokon shugaban kasa ya kawo masa agaji.
Wannan Bawan Allah da ya bayyana sunansa da Sani Adamu ya roki shugaba Muhammadu Buhari da iyalinsa da su taimaka masa da abin da zai ci a wannan watan na azumi.
Sani Adamu ya yi ikirarin tsohon soja ne shi wanda ya yi aiki da shugaban kasar mai-ci tun shekarar 1964 a lokacin Muhammadu Buhari ya na Legas, har ya fadi lambarsa ta aiki.
A cewar dattijon ya yi irin wannan kuka a baya, kuma mai dakin shugaban kasar da wata ‘yaruwarta da ke jami’a su ka kawo masa gudumuwar abinci da tufafi da kudi N50, 000.
Sai dai an yi masa alkawarin gyara masa gidansa da ya ruguje amma har yanzu shiru. Adamu ya ce kwamishinar harkar cikin-gida na Borno, ya gana da shi amma bai yi masa komai ba.
KU KARANTA: Alkalin Alkalan Jihar Yobe ya kwanta dama a watan Azumi
Tsohon sojan ya yi kukan girma ya zo masa kuma yaronsa ya mutu a bariki, bayan haka kuma kudinsa na aiki ba su fito ba, don haka ya nemi ya aikawa shugaban kasar sako ta bidiyo.
Dattijon ya ce idan shugaban kasar ko iyalinsa sun tashi aiko masa da taimako, a tuntubi wani mutumi mai suna Alhaji Rabiu Ibrahim Maisiga, da ke Bulunkutu, a garin Maiduguri a Borno.
A cewar Sani Adamu, shi ne wanda ya rika kai yaran Muhammadu Buhari makaranta a yayin da ya ke gwamna a lokacin mulkin soji. Buhari ya yi gwamna ne a tsohuwar jihar Borno a 1975.
Kawo yanzu Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an kalli wannan bidiyo fiye da sau 12, 000. An kuma yi dace wani daga cikin hadiman shugaban kasar ya sa idonsa kan sakon da dattijon ya aika.
Bashir Ahmad wanda shi ne mai taimakawa Buhari wajen harkokin kafafen sadarwa na zamani, ya nuna cewa za ayi abin da ya dace. Ta’alikin ya yi wa shugaban addu'ar cin nasara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng