An yi gwajin sabon maganin cutar korona a kan mutane 45

An yi gwajin sabon maganin cutar korona a kan mutane 45

A yayin da masana kimiya a fadin duniya ke ci gaba da rige-rigen samar da riga-kafin cutar korona, wani kamfanin kera magunguna na kasar Amurka, Moderna, ya cimma wani munzali na nasara.

Kamfanin Moderna mai tushe a jihar Massachusetts ta Amurka, ya kera wani sabon maganin cutar korona, sai dai kuma ya yi gwajin sa ne a kan mutane 'yan kalilan.

Sakamakon gwajin da aka gudanar a kan mutane 45 bayan shan maganin da suke kiran shi da suna mRNA-1273, ya nuna cewa jikinsu ya samu riga-kafin kwayar cutar korona.

A cewar kamfanin Moderna, maganin mRNA-1273, wanda aka kirkira cikin matakai uku na nauyi daban-daban, an baiwa mutane 45 kuma dukkansu sun samu garkuwa da riga-kafin cutar korona.

Sai dai mutane takwas da aka baiwa maganin a kan nauyin micrograms 25 da 100 a watan Maris, jikinsu ya fi nuna mafi kyawun karbuwa da gamsuwa da tasirin maganin.

Jikin mutanen takwas ya samar da ingantacciyar garkuwa wadda ta yi daidai da garkuwar da ake samu a jikin mutanen da suka kamu da cutar korona kuma suka warke.

An yi gwajin sabon maganin cutar korona a kan mutane 45
An yi gwajin sabon maganin cutar korona a kan mutane 45
Asali: UGC

Cikin rahoton wanda aka watsa a shafin yanar gizo na WebMD a daren ranar Litinin, kamfanin Moderna ya ce ya kammala shirin ci gaba zuwa mataki na biyu domin tabbatar da ingancin maganin.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, za a ci gaba da gwajin maganin a kan mutane masu yawa a wannan shekara domin samun tabbaci.

KARANTA KUMA: 'Yan fashi a jirgin sama sun kai hari kauyukan Neja, sun kashe fasto, makaho, da wasu mutum 3

Wannan sabon magani yana amfani da wani abu da ake kira da tsarin isar da sakonni na RNA, wato sunadarin da ke jikin dukkanin abubuwa masu rai kuma ba ya bukatar kwayoyin cututtuka wajen kirkirarsa.

"Ina tsammanin gamayyar ilimin kimiyya na nuna mana cewa wannan sabon magani mai ba da ingantacciyar kariya irin haka, shi ne riga kafin cutar korona," in ji Tal Zaks, shugaban kwararrun kiwon lafiya na kamfanin Moderna.

An yi wannan gwajin ne ta hanyar hadin kai da Cibiyar Kiwon Lafiyar ta Kasa da kuma Cibiyar Kula da Cututtuka masu Yaduwa.

Sai dai sa'annin juna a bangaren kiwon lafiya ba su yi nazari a kansa ba kuma ba a buga shi a wata mujjalar kiwon lafiya ba.

A halin yanzu dai akwai akalla magungun 60 na cutar korona da ake ci gaba da gudanar da gwaji a kansu, kuma an yi gwajin shida daga cikinsu a kan mutane domin samun tabbaci a kan ingancinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng