Sojojin kasar Nijar ke taimakonmu, na Najeriya sun yi watsi da mu - Sanata Gobir

Sojojin kasar Nijar ke taimakonmu, na Najeriya sun yi watsi da mu - Sanata Gobir

Sanatan jam'iyyar APC da ke wakiltar mazabar jihar Sokoto ta Gabas, Ibrahim Gobir, ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun gaza wajen ceton jama'arsa daga 'yan bindigar da su ka addabesu da yawan kai hare - hare yankin.

Gobir ya bayyana hakan ne ranar Talata a zauren majalisar dattijai yayin da majalisar ke tattaunawa a kan umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bawa rundunar soji na share 'yan bindiga daga jihar Katsina.

Sanatan ya bayyana cewa yanzu haka jama'arsa sun dogara ne da sojojin kasar Nijar domin samun ceto duk lokacin da 'yan bindiga su ka kai musu hari.

"Babu tsaro ga jama'ata a gabashin jihar Sokoto a yayin da 'yan bindiga ke cigaba da kai musu hari ba kakkautawa.

"An kashe ko kuma an sace a kalla mutane 300 a cikin watanni uku da su ka gabata, sannan an sace Shanu fiye da 5,780 wanda darajar kudinsu ta kama biliyan N2.5.

"Mun mika kukanmu ga gwamnatin tarayya ta hannun majalisar dattijai.

Sojojin kasar Nijar ke taimakonmu, na Najeriya sun yi watsi da mu - Sanata Gobir

Sojojin kasar Nijar ke taimakonmu, na Najeriya sun yi watsi da mu - Sanata Gobir
Source: UGC

"Yanzu mun dogara ne da sojojin kasar Nijar a duk lokacin da 'yan bindiga su ka kai hari saboda sojojin Najeriya sun yi watsi da mu.

"Duk lokacin da aka kawo hari sai an kira sojojin Najeriya da ke da kusanci da yankin, amma ba za su amsa a kan lokaci ba.

DUBA WANNAN: Korona a Najeriya damfara ce kawai, wasan kwaikwayon da ba a tsara shi da kyau ba - Mai jinyar da aka sallama

"Sojojin kasar Nijar ba sa bata lokaci wajen kawo ma na dauki duk lokacin da aka kirawosu duk da nisan da su ke da shi daga yankin.

"A yanzu haka, maganar da na ke yi, mutanen gabashin jihar Sokoto sai hijira su ke yi zuwa yankunan kasar Nijar saboda an kasa ba su tsaro a Najeriya," a kalaman sanata Gobir.

Majalisar dattijai ta yabawa shugaba Buhari a kan umarnin da ya bayar na share 'yan bindiga daga jihar Katsina.

Sai dai, majalisar ta ce kamata ya yi umarnin ya hada da jihohin Zamfara, Kaduna, Neja, Sokoto da sauran jihohin da ke fama da hare - haren 'yan bindiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel