Kashi 51% na duk masu cutar korona sun kasance a kananan hukumomi 9 na Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Kashi 51% na duk masu cutar korona sun kasance a kananan hukumomi 9 na Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, kashi 51 cikin 100 na duk adadin masu cutar korona a Najeriya sun kasance a wasu kananan hukumomi 9 kacal da ke fadin kasar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan da cewa kananan hukumomi 9 a Najeriya sun tattare kashi 51 cikin 100 na duk masu cutar korona a kasar.

Sanarwar Sakataren Gwamnatin ta zo ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai kan halin da kasar ta ke ciki game da annobar korona.

Boss Mustapha wanda ya kasance shugaban kwamitin kula da annobar korona a Najeriya, ya ce bincikensu ya gano cewa, wasu kananan hukumomi 9 a fadin Najeriya sun dauke nauyin duk wani adadi na masu cutar korona a kasar.

Yayin tabbatar da cewa kananan hukumomin 9 suna da kashi 51% na adadin masu cutar korona a duk fadin Najeriya, ya kuma ce dukkaninsu na da dimbin al'umma mai yawan gaske.

Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha
Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha
Asali: UGC

Ya kuma lura cewa an inganta tsarin kiwon lafiya da kayan aiki don lalube da gwaji, gami da killace wadanda cutar korona ta harba.

KARANTA KUMA: An yi gwajin sabon maganin cutar korona a kan mutane 45

Haka kuma Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC), ta sanar da cewa karin sabbin mutane 216 ne aka tabbatar da sun kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin 11:53 na daren ranar Litinin a shafinta na Twitter, ta ce an samu karin sabbin mutane 216 da suka kamu a wasu jihohi goma na Najeriya

NCDC ta fitar da jerin jihohi da jimillar sabbin wadanda cutar ta harba a kowacce jiha kamar haka: 74-Lagos, 33-Katsina, 19-Oyo, 17-Kano, 13-Edo, 10-Zamfara, 8-Ogun, 8-Gombe, 8-Borno, 7-Bauchi, 7-Kwara, 4-FCT, 3-Kaduna, 3-Enugu, 2-Rivers.

A halin yanzu alkaluman NCDC sun tabbatar da cewa kawo yanzu, akwai jimillar mutane 6175 da aka tabbatar sun harbu da kwayoyin cutar korona a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel