Tashin Hankali: Guguwa Mai Karfi Ta Hallaka Mutane, Ta Yi Mummunar Barna a Yobe

Tashin Hankali: Guguwa Mai Karfi Ta Hallaka Mutane, Ta Yi Mummunar Barna a Yobe

  • Akalla mutane uku ne suka rasu, wasu da dama suka jikkata bayan wata guguwa mai ƙarfi ta afkawa garin Gashua da ke jihar Yobe
  • Guguwar ta lalata ɗaruruwan gidaje, shaguna, turakun wutar lantarki da na kamfanonin sadarwa, ta bar iyalai da dama ba matsuguni
  • Hukumar YOSEMA ta fara tantance barnar da wannan guguwa ta yi wa al'umma, domin kai agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yobe - Akalla mutum uku sun rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wata guguwa mai ƙarfi da ta afkawa garin Gashua, hedikwatar ƙaramar hukumar Bade ta jihar Yobe.

Mazauna yankin sun shaida cewa guguwar, wadda ta yi kusan mintuna 30 tana kaɗawa a yammacin ranar Laraba, ta lalata ɗaruruwan gidaje, shaguna, turakun kamfanonin sadarwa da na wutar lantarki.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Guguwa mai karfi ta hallaka mutane 3, an yi asarar dukiya mai yawa a Yobe
Wasu mutane suna duba gidajen da suka ruguje bayan wata guguwa mai karfin gaske a Bauchi. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Barnar da guguwa ta yi a Yobe

Wannan mummunan iftila'i ya sanya iyalai da dama sun rasa muhallansu tare da haddasa asarar dukiyoyi ta miliyoyin naira, in ji rahoton Daily Trust.

Wani mazaunin garin Gashua mai shekara 65, Aminu Muhammad, ya ce wannan na ɗaya daga cikin mafi munin bala'o'in da ya taɓa gani a rayuwarsa.

Ya ce mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da gidaje da hanyoyin samun abin masarufi na mutane da dama suka lalace sakamakon guguwar.

A cewarsa, sare bishiyoyi ba tare da tsari ba na iya kasancewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara muni ga tasirin guguwar, domin bishiyoyi kan taimaka wajen rage ƙarfin iska.

Shugaban ƙaramar hukumar Bade, Ibrahim Babagana Yurema, ya tabbatar da cewa mutum uku sun mutu, yayin da wasu ke karɓar magani a Asibitin Kwararru na Gashua.

Mutane sun yi asarar gidaje da motoci

Ɗaya daga cikin waɗanda guguwar ta shafa, Abdulhadi Ibrahim Gashua, ya bayyana cewa rufin gidansa ya tashi gaba ɗaya, yayin da motarsa ta samu mummunar illa.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu za ta tara matan Kano ta ba su tallafin kayan sana'a

Ya ce wasu sassa, ciki har da fitilar gaban motarsa sun lalace, sannan na'urorin samar da lantarki daga hasken rana da ke saman gidansa sun lalace.

Ya ƙara da cewa duk da irin asarar da ya yi, yana godiya da cewa babu wani daga cikin iyalansa da ya ji rauni.

Shi ma wani mazaunin yankin, Yahaya Mato, ya ce duk da cewa ruwan sama bai yi yawa ba, iska mai ƙarfi ce ta haddasa babbar barna a faɗin garin.

Ya bayyana cewa wasu turakun kamfanonin sadarwa sun faɗi, wasu kuma sun samu matsala, yana mai danganta hakan da raguwar bishiyoyi saboda noma da faɗaɗa gine-gine, in ji rahoton Punch.

Guguwa mai karfi ta yi barna a Yobe, mutane sun rasa rayukansu
Taswirar jihar Yobe, inda guguwa ta hallaka mutane 3 ta lalata kadarori. Hoto: Legit.ng
Source: Original

YOSEMA ta fara tantance barnar

Daraktan bincike da ceto na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YOSEMA), Dr Ibrahim Muhammad Jalo, ya ce hukumar ta fara tantance irin barnar da guguwar ta yi.

Ya bayyana cewa iftila'in ya shafi wasu sassan ƙananan hukumomin Yunusari da Bursari, inda aka tura jami'ai da masu aikin sa kai domin gudanar da binciken gaggawa.

Ya tabbatar da cewa bayan kammala tantance barnar, hukumar za ta fara raba agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa bisa ga irin buƙatar da suka fi gaggawa.

Kara karanta wannan

PDP ta yi kaca kaca da gwamnatin Gombe kan zargin bai wa mawakin Kano N315m

Guguwa ta yi barna a jihar Jigawa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Guguwa mai karfin gaske ta rutsa kauyuka da dama a Jigawa, inda ta kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu fiye da 50.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ibtila'in ya shafi gidaje 5,403 a cikin kauyuka 120 da ke kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da sakin kudade tallafi cikin gaggawa domin taimakawa wadanda bala'in ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com