Kasar Musulunci Ta Iran ba Za Ta Mika Wuya ba, Ta Shirya Komawa Yaƙi da Amurka

Kasar Musulunci Ta Iran ba Za Ta Mika Wuya ba, Ta Shirya Komawa Yaƙi da Amurka

  • Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma jagoran tawagar tattaunawar sulhu ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa miƙa wuya ga Amurka ba
  • Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi barazanar martani idan Amurka ta karya yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu
  • Wani masani ya ce har yanzu akwai yiwuwar a farfaɗo da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Shugaban Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani a tattaunawar ƙasar, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta taɓa mika wuya ga Amurka ba.

Ghalibaf ya jaddada cewa rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ba zai taɓa ƙarewa ba matukar sai kasar musulunci ta mika wuya.

Mojtaba.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da makami mai linzami da aka harba Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A rahototn tashar Al-Jazeera, Ghalibaf ya ce Iran a shirye take ta kare kanta idan Amurka ta karya yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Iran ta nuna yatsa ga Donald Trump, ta harba makamai kan Kuwait da wasu kasashe 2

Iran ta shirya komawa yaki da Amurka

Ya ce:

"A duk lokacin da Amurkawa suka karya wannan yarjejeniya, muna shirye mu kare kanmu gaba ɗaya, kuma za mu tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin al'ummar Iran."

Ya ƙara da cewa kawo ƙarshen yaƙi na da muhimmanci ga ƙasashen duniya, amma ya jaddada cewa hakan ba zai kasance ta hanyar Iran ta miƙa wuya ba.

"Kawo ƙarshen yaƙi abu ne mai muhimmanci ga ƙasashen duniya, amma kowa ya sani cewa wannan rikici ba zai ƙare da Iran ta miƙa wuya ba," in ji shi.

Ghalibaf ya kuma yi kira ga ƙasashen Musulmi da su haɗa kai tare da nuna juriya kan Amurka da Isra'ila, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.

Za a iya farfaɗo da yarjejeniyar?

A nasa ɓangaren, babban masanin harkokin tsaro a cibiyar RUSI, Michael Stephens, ya bayyana cewa har yanzu akwai yiwuwar a dawo da yarjejeniyar MoU tsakanin Iran da Amurka, sai dai hakan zai buƙaci himma daga ɓangarorin biyu.

Kara karanta wannan

"Za mu rama sau 20"; Shugaba Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran

Stephens ya ce babban abin damuwarsa shi ne yadda kowanne ɓangare ya ƙi amincewa cewa ɗayan na da wata hujja.

"Abin da ke damuna shi ne babu wani ɓangare da ke amincewa cewa ɗayan na da wata hujja. Idan ana son diflomasiyya ta yi nasara, dole ne wani ya karya wannan tangarɗar."
Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi ga manema labarai kan yakin Iran Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Ya kuma bayyana cewa komawa fagen yaƙi abu ne da ake iya tsammani saboda yadda aka tsara yarjejeniyar.

A cewarsa, Iran ta samu wasu fa'idoji tun farkon yarjejeniyar, amma daga baya Amurkqa ta yi ƙoƙarin janye wasu daga cikinsu.

Iran za ta dauki fansar kisan Khamenei

Kun ji cewa babban kwamandan IRGC, Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya ce za aNdauki fansa kan Amurka da Isra'ila saboda kashe Ayatollah Ali Khamenei.

Vahidi ya ce kisan Khamenei ba zai taba gogewa daga tarihin al'ummar Musulmi da bangaren gwagwarmaya musamman a kasar Iran ba.

Ya kara da cewa shugabannin Amurka da sauran makiyan Juyin Juya Halin Musulunci kada su yi zaton cewa kashe jagoran zai karya ruhin gwagwarmaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262