Masu bincike na kokarin gano maganin cutar Coronavirus a Jami’ar kasar Sin

Masu bincike na kokarin gano maganin cutar Coronavirus a Jami’ar kasar Sin

Rahotanni daga gidan yada labarai na AFP sun bayyana cewa ana kyautata zaton samun maganin da zai kai ga kawo karshen annobar cutar COVID-19 a wani dakin bincike a Sin.

Wasu masana da ke aiki a dakin nazarin jami’ar Perking a birnin Beijing su na kokarin gano maganin da zai taimaka wajen rage tasirin COVID-19 da kuma ba jiki garkuwa daga cutar.

AFP ta ce kasar Sin inda cutar ta fito a karshen bara ta na kokarin nemowa Duniya maganin da zai kashe kwayar cutar. A halin yanzu kasashe su na faman tseren binciko maganin ciwon.

Idan an yi nasarar samun wannan magani, lokacin da ake dauka wajen jinyar COVID-19 zai ragu, haka zalika za a rika amfani da maganin a matsayin rigakafi ga wadanda ba su harbu ba.

Darektan cibiyar da ke da alhakin bincike a jami’ar ta Beijing, Sunney Xi, ya shaidawa AFP cewa an yi nasarar yi wa dabbobi gwajin wannan magani, inda aka yi amfani da wasu beraye.

KU KARANTA: An jarraba wnai maganin COVID-19 a kan wasu mutane a Amurka

Sunney Xi ya ce karfin kwayar COVID-19 ya ragu da su ka jarraba aikin wannan magani a jikin berayen. An samo sinadaran maganin ne daga jinin wasu mutane 60 da yanzu sun warke.

Mista Xi ya ce sun yi farin ciki da su ka fahimci cewa fasaharsu za ta iya kawar da kwayar Coronavirus. Xi ya ke cewa za a iya samun wannan magani a kasuwa a karshen shekarar nan.

“Shirin gwajin maganin ya fara kankama, za mu jarraba maganin ne a kasar Australiya tun da yanzu an samu raguwar masu kamuwa da cutar a Sin." Ya ke bayyanawa manema labarai.

A kasar Sin, akwai kwayoyi biyar da ake bincike a kansu da nufin yakar cutar nan ta COVID-19. Wadannan bincike sun kai matakin da yanzu za a fara shirin yin gwaji a jikin Bil Adama.

Hukumar lafiya ta Duniya ta WHO ta na ganin cewa kafin a iya gano maganin wannan cuta, sai an shafe akalla shekara guda zuwa shekara guda da rabi, akasin ra’ayin wasu masu bincike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel