COVID-19: Za a tura 'Yan Hisbah masallatai da filayen Idi a Kano

COVID-19: Za a tura 'Yan Hisbah masallatai da filayen Idi a Kano

Don tabbatar da cewa an bi sharruda da dokokin takaita yaduwar korona a masallatan Jumaa da aka bawa izinin bude wa a ranar Sallar Idi, gwamnatin Kano ta yi alkawarin aike wa da 'Yan Hisbah zuwa masallatai.

Sauran sharrudan da aka gidayawa mutanen jihar kafin bude masallatan sun hada da saka takunkumi da bayar da tazara a cewar kwamishinan labarai, Muhammad Garba.

Sai dai kafin masallata su shiga masallatan sai sun wanke hannun su da man kashe kwayoyin cuta wato hand sanitizer kuma a tabbatar an tsaftace harabar masallatan.

COVID-19: An aike da 'Yan Hisbah masallatai da filayen Idi a Kano. Hoto daga Daily Nigerian

COVID-19: An aike da 'Yan Hisbah masallatai da filayen Idi a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hare-haren 'yan bindiga: Matasa a Katsina sun rufe babban titin da ta sada Najeriya da Nijar

Kwamishinan ya ce a yunkurin ta na sassauta dokar kulle a jihar da kwamitin kar ta kwana na COVID-19 na gwamnatin tarayya ta saka na sati biyu, gwamnatin jihar ta fitar da wasu sharruda na sassauta dokar.

Cikin sanarwar da Garba ya fitar bayan taro da kwamitin malamai da sauran masu ruwa da tsaki a jihar a daren ranar Litinin, ya ce gwamnatin jihar ta san mawuyancin halin da mutane ke ciki hakan yasa aka sassauta dokar.

Ya ce bayan taron da aka gudanar da kwararru a fanin lafiya, malamai da sauran masu ruwa da tsaki, gwamnatin jihar da dauki wasu matakai domin dakile yaduwar cutar a jihar wadda hakan yasa aka sassauta dokar a ranakun Lahadi, Laraba da Juma'a daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana.

Garba ya ce Ganduje ya umurci Hukumar Hisbah ta yi taro da limamai kana ta aike da jami'anta zuwa masallatan Jumaa a dukkan fadin jihar don tabbatar da cewa masallata sun bi sharrudan da aka gindaya musu

Sharrudan sun hada daa bayar da tazara tsakanin mutane, wanke hannu sa sabulu ko handa sanitizer da saka takunkumin fuska.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin ta amince a bawa mutane damar yin sallar Idi a dukkan masarautu biyar na jihar inda za a sassauta dokar hana fita daga karfe 6 na safe zuwa karfe 2 na rana.

Garba ya bayyana cewa ba za a gudanar da bukukuwan sallah ba a dukkan masarautun jihar biyar kamar ziyarar Gidan Shettima, Hawan Daushe, Hawan Nassarawa da Hawan Dorayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel