Coronavirus: An fi samun yawan mace-mace a Legas, Kano da Borno - Mamora

Coronavirus: An fi samun yawan mace-mace a Legas, Kano da Borno - Mamora

Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske a kan halin da kasar nan take ciki game da annobar cutar korona wadda ta yi wa duk wani kwararo da sako lullubi a fadin duniya.

Gwamnatin kasar ta ce an fi samun yawan mace-macen mutane sanadiyar annobar korona a wasu jihohi uku na kasar da suka hadar da Legas, Borno da Kano.

Karamin Ministan Lafiya, Adeleke Olorunnimbe Mamora, ya ce kashi 52 cikin 100 na mace-macen da aka samu a kasar sanadiyar cutar korona sun tattara ne a jihohin Kano, Borno da kuma Legas.

Sanarwar da Mista Mamora ya yi a ranar Litinin ya kuma ce kashi 60 cikin 100 na wadanda cutar korona ta harba a fadin kasar nan sun kasance 'yan tsakanin shekarun haihuwa daga 21 zuwa 50.

Ya zuwa daren ranar Litinin, an samu mutum 6175 da cutar korona ta harba a duk fadin kasar kamar yadda alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa NCDC ta sanar.

Har ila yau dai jihar Legas ce a kan sahu na gaba da mafi yawan adadin masu cutar korona a duk cikin jihohin Najeriya.

Karamin Ministan Lafiya; Adeleke Olorunnimbe Mamora
Karamin Ministan Lafiya; Adeleke Olorunnimbe Mamora
Asali: UGC

Jihar ta na da mutum 2,624 da NCDC ta tabbatar sun kamu da cutar, sai kuma jihar Kano da ta biyo baya da mutum 842, sannan kuma birnin tarayya Abuja a mataki na uku da mutum 422. Jihar Borno da take a mataki na biyar tana da mutum 223.

KARANTA KUMA: Kaso 51% na duk masu cutar korona sun kasance a kananan hukumomi 9 na Najeriya - Gwamnatin Tarayya

Haka kuma Gwamnatin ta bayyana cewa, kaso 51 cikin 100 na duk adadin masu cutar korona a Najeriya sun kasance a wasu kananan hukumomi 9 kacal da ke fadin kasar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan bayan zaman karin haske kan cutar korona kashi na 33 tare da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Villa.

Sanarwar Sakataren Gwamnatin ta zo ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai kan halin da kasar take ciki game da annobar korona.

Boss Mustapha wanda ya kasance shugaban kwamitin kula da annobar korona a Najeriya, ya ce bincikensu ya gano cewa, wasu kananan hukumomi 9 a fadin Najeriya sun dauke nauyin duk wani adadi na masu cutar korona a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel