Shugaba Buhari ya aika ma majalisa sunan Yuguda don nada shi muhimmin mukami

Shugaba Buhari ya aika ma majalisa sunan Yuguda don nada shi muhimmin mukami

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sunan Lamido Yuguda ga majalisar dattawan Najeriya don su amince da shi kafin ya nada shi wani muhimmin mukami a gwamnatinsa.

Punch ta ruwaito shugaban kasa Buhari na da burin nada Lamido Yuguda a matsayin babban daraktan hukumar zuba hannun jari ta Najeriya, watau Securities and Exchange Commission.

KU KARANTA: Annobar Corona: Za a iya gudanar da sallar Idi a gida – Malaman kasar Saudiyya

Mashawarci na musamman ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, Ezrel Tabiowo ne ya bayyana haka a ranar Talata, 19 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya aika ma majalisa sunan Yuguda don nada shi muhimmin mukami
Ofishin SEC Hoto: ThisDaylive
Asali: UGC

Tabiowo ya kara da cewa baya ga sunan Yuguda, haka zalika shugaba Buhari ya tura ma majalisar sunayen mutane uku da yake so a nada su mukaman kwamishinoni a hukumar.

Wadannan sunaye sun hada da; Ibrahim Boyi, cikakken kwamishina, Reginald Karawusa, cikakkiyar kwamishina da kuma Obisan Joseph, shi ma a matsayin cikakken kwamishina.

Wasikar shugaban kasa ta bayyana cewa: “Duba da sashi na 3 da 5 (1) na dokar zuba hannun jari da tsaro na shekarar 2007,

“Na rubuta wannan wasikar don neman amincewar majalisar dattawa da nadin mutanen nan guda hudu a matsayin babban daraktan SEC da kwamishinoni. Ga takardun bayanan karatunsu da ayyukan su nan a tare da wasikar.” Inji Buhari

Mista Tabiowo yace Ahmad Lawan ya karanta wasikar shugaba Buhari ne a yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A yanzu haka hukumar na karkashin shugabancin Mary Uduk ne, wanda kwanakin baya aka zarge ta da daukan ma’aikata 811 daga jaharta ta Anambra, amma ta dauki 1 daga Kano.

Sai dai Uwargida Uduk ta musanta wannan zargi, inda tace tun da ta hau kujerar shugabancin SEC a matakin wucin gadi bata dauki ko mutum daya aiki ba.

A wani labarin kuma, Babban akanta na kasa ya bayyana dalilin da yasa Malaman jami’a1,180 basu samu albashin su na watan Maris ba, duk da umarnin da shugaba Buhari ya bayar.

Idris ya bayyana haka ne ta bakin daraktan watsa labaru na ofishinsa, Henshaw Ogubike, inda yace malaman sun gaza cika sharuddan BVN ne da ofishin ta gindaya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel