Annobar Corona: Za a iya gudanar da sallar Idi a gida – Malaman kasar Saudiyya
Gwamnatin Saudiyya ta umarci jama’an kasar su gudanar da sallar Idin bana a gidajensu bayan samun fatawar majalisar malamai ta kasar.
BBC ta ruwaito shugaban majalisar Malaman kasar dake bada fatawa, Abdul Aziz Asheikh ne ya sanar da haka, inda yace ya halasta a yi Idi a gida duba da annobar da ake fama da ita.
KU KARANTA: Duk da dokar Buhari, Ganduje ya baiwa Kanawa daman sallar Idi da sallar Juma’a
Haka zalika Shehin Malamin ya bayyana cewa ita ma zakkar fidda kai ba sai an bi gida gida ba duba da dokar zaman gida da aka sanya,za a iya bayarwa ta hannun kungiyoyin bayar da agaji.
Sallar Idi ana yin ta ne a ranar farko ta watan Musulunci na Shawwal, kuma raka’a biyu ce da ake ma raka’ar farko kabarbari guda 6, sai kabarbari 5 a raka’a ta biyu, sai huduba bayan an idar.
Sai dai a wannan karon, duba da hali na musamman da annobar Coronavirus ta jefa duniya, Asheikh yace ana iya yin sallar ba tare da an gudanar da huduba ba.
Bugu da kari, shi ma wani babban Malamin kasar Saudiyya, Abdullah Al-Sulaiman ya bayyana cewa sallar Idi ta yi daidai idan aka yi a jam’i ko kuma mutum daya kacal
“Misali da sahabin Annabi mai suna Anas Bin Malik yake gidansa a Zawiya bai samu inda ake yin jam'in Idi ba sai ya yi sallar a gida da iyalansa da kuma mai yi masa hidima Abdullah Bin Abi Otba.”inji shi.
Tun bayan barkewar Coronavirus ne kasar Saudiyya ta dauki tsauraran matakai don gudun yaduwar cutar da suka hada da dakatar da aikin Umarah da shiga Masallatai.
A yanzu haka akwai mutane 57,345 da suka kamu da cutar a kasar, yayin da 28, 748 suka warke, sai kuma 320 da suka rigamu gidan gaskiya a dalilin cutar.
A wani labarin kuma, mu ma a nan Najeriya, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa a Masallatan Juma’a za’a gudanar da sallar Idi a bana.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin ganawa da wasu shuwagabannin al’ummar jahar Sakkwato da suka kai masa ziyara dangane da batun sallar Idin bana.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng