Abin da yasa Malaman Jami’a 1,180 basu samu albashin su ba – Babban akanta Ahmad

Abin da yasa Malaman Jami’a 1,180 basu samu albashin su ba – Babban akanta Ahmad

Babban akanta na kasa, Ahmad Idris ya bayyana dalilin da yasa Malaman jami’a da yawansu ya kai 1,180 basu samu albashin watan Maris ba, duk da umarnin da shugaba Buhari ya bayar.

Idris ya bayyana haka ne ta bakin daraktan watsa labaru na ofishinsa, Henshaw Ogubike, inda yace malaman sun gaza cika sharuddan BVN ne da ofishin ta gindaya.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya bayyana ma Musulmai inda zasu gudanar da sallar Idin bana

Henshaw ta ce an samu bambanci a sunayen Malaman da kuma sunayen dake asusun bankunan su, don haka aka samu tsaiko wajen biyansu albashin.

Abin da yasa Malaman Jami’a 1,180 basu samu albashin su ba – Babban akanta Ahmad

Kungiyar ASUU Hoto: Facebook
Source: UGC

“Dole ne ma’aikata su gyara sunayensu yayi daidai da sunan da suke amfani da shi a asusun bankinsu, bugu da kari manhajar IPPIS ba ta yarda da asusun da mutane biyu ko uku ke amfani da ita ba, dole ne kowa ya mallaki asusun sa.

“Ta BVN ne kawai za mu iya tabbatar da dukkanin lambobin asusun bankunan da jami’o’I suka turo mana, mu kuma za mu aikasu ga hukumomin gwamnati da suka dace don tantancewa.

“Ta haka ne malamai 1,180 suka gaza tsallake gwajin BVN, kuma tuni mun aika ma jami’o’I sunayensu domin su yi gyaran daya kamata.” Inji ta.

Haka nan akantan ya yi bayani game da zaftare albashin malamai, inda yace harajin PAYE, kuma sashi na 34 na dokar harajin kudin shiga ne ta tanadi haka, da kuma wasu harajin da aka cire.

“Kafin zuwan IPPIS, jami’o’I basa cire harajin daya kamata su cire, suna tafka kuskure, hakan yasa malamai basa biyan cikakken harajin PAYE, haka kuma akwai harajin gida wanda ya lashe kashi 2.5 na albashin.

“Shi ma dokar majalisar dokokin Najeriya ce ta samar da shi don tabbatar da ma’aikata zasu iya karbar bashi domin su samu daman mallakan gidansu na kansu, kuma idan mutum bai amsa ba za’a mayar masa da kudinsa da kudin ruwan da suka tara bayan ya yi ritaya.” Inji shi.

Babban akantan yace bukatar ASUU shi ne a cire su daga biyan wadannan kudade, ko kuma a basu zabi, sai dai yace ba hurumin IPPIS bane wannan, hurumin majalisa ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel