COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna

COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna

An kama Janar din Soja a jihar Kaduna bayan an same shi da laifin karya dokar kulle da gwamnatin jihar ta saka saboda dakile yaduwar coronavirus.

Kwamishinan sharia na jihar, Aisha Dikko ce ta sanar da hakan a ranar Litinin 18 ga watan Mayu kamar yadda LIB ta ruwaito.

Ta ce an kama sojan ne sanye da kayansa na aiki yana tuki tare da wasu fasinjoji uku a cikin mota daga Abuja kuma ba su sanye da takunkumin rufe fuska.

An yi masa sharia an kuma same shi da laifin saba dokar zama a gida da kuma rashin sanya takunkumin fuska.

DUBA WANNAN: PDP ta dakatar da Hunkuyi, Dogara da wasu 'ya'yanta 5

COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna

COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna. Hoto daga Channels TV
Source: UGC

Dikko ta ce;

"Janar din ya fadi sunansa kuma ya ce ya taso daga Abuja ne inda ya ke yin aiki.

"Sai dai kotun ta yi sharia ga sauran fasinjoji ukun kuma an same su da laifin saba dokar zaman gida da rashin sanya takunkumin fuska."

Har wa yau, rahotanni sun nuna cewa an kama sanannen malamin addinin musulunci, Yusuf Rigachikun da dansa saboda saba dokar kule da aka sa saboda COVID-19.

Malamin da aka kama a mahadar jamiar Kaduna, KASU, ba tare da takunkumin fuska ba ya ce gidan rediyon Kaduna, KSMC, ce ta gayyace shi don yin wani shiri.

Kwamishinan ta kara da cewa; "An tuhumi Rigachikun da dansa da laifin rashin sanya takunkumin fuska an kuma ci su tarar N5000 kowanensu.

"An kuma bukaci malamin ya yi wa alumma hidima ta hanyar wayar da kan mutane hanyoyin da za su bi don kare yaduwar COVID-19.”

Dikko ta gargadi mutanen jihar su dena karya dokar da hana fita inda ya kara da cewa an yanke wa mutum 75 hukunci cikin 105 da aka kama da laifin karya dokar hana shigowa jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel