Armaya’u Hamisu Bichi ne sabon Shugaban Jami’ar FUDMA – Adamu Adamu

Armaya’u Hamisu Bichi ne sabon Shugaban Jami’ar FUDMA – Adamu Adamu

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da nadin Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi a matsayin shugaban jami’ar tarayya da ke garin Dutsinma, a jihar Katsina.

A wata takarda da ta fito daga ofishin mai girma ministan ilmin Najeriya, Malam Adamu Adamu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan nadi da aka yi a cikin watan nan.

Takardar da Malam Adamu Adamu ya aikowa Armaya’u Hamisu Bichi a ranar 15 ga watan Mayu, 2020, ta shigo hannumu. Farfesan zai yi shekaru biyar ya na juya akalar jami’ar ta Dutsinma.

Ko da cewa takardar da ta shiga hannun Armaya’u Hamisu Bichi a ranar Juma’ar da ta gabata ne, ministan ya ce wa’adin sabon shugaban jami’ar ya kankama tun a ranar 12 ga watan Mayu.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an karawa tsohon mukaddashin shugaban jami’ar ta FUDMA, Dr. Babangida Umar Dangani a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon watanni shida.

KU KARANTA: Buhari ya nada Kashim Ibrahim - Imam a TETFUND - Ministan ilmi

Armaya’u Hamisu Bichi ne Shugaban Jami’ar FUDMA – Adamu Adamu

Armaya’u Hamisu Bichi zai canji Dr. Babangida Dangani a FUDMA Hoto: Twitter
Source: Twitter

Farfesa Bichi ba bakon jami’ar tarayyar ta Dutsinma ba ne domin kuwa a baya ya taba rike shugabancin makarantar na rikon kwarya, a wancan lokaci ba a tabbatar da shi a kujerar ba.

Ana sa rai Bichi zai sauka daga kan wannan mukami ne a watan Mayun 2025. Yanzu an yi canjin shugabanni kusan sau shida kenan a jami’ar tarayyar daga watan Maris na 2016 zuwa yau.

Bayan tafiyar farfesa James Ayatse ne shugaban kasa ya nada farfesa Abdu Haruna Kaita, wanda bayan shekara guda majalisar jami’ar a karkashin shugaba Dr. Marliya Zayyana ta tsige shi.

Bayan sauke Abdu Haruna Kaita ne aka nada Armaya’u Bichi wanda ya yi shekaru kusan biyu da rabi. Sai kuma a farkon 2019 aka nada Aminu Kankia a matsayin shugaban rikon kwarya.

Bayan wani ‘dan lokaci dole farfesa Kankia ya bar wannan kujera. Wannan ya jawo aka zabi farfesa Adamu Nchama Baba-Kutigi, bayan wata shida ya ba Dr. Babangida Dangani wuri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel