Sarkin Zazzau Ya Bayar da Shawara kan Gudanar da Sahihin Zabe a Najeriya
- Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya bukaci a rika amfani da na'ura wajen kada kuri'a a duk zabubbukan Najeriya
- Ya ce amfani da fasaha zai kara inganta sahihanci, gaskiya da saurin gudanar da zabubbuka a kasar nan
- Mai martaba sarkin ya a bayyana cewa gogewarsa daga China, Brazil da Amurka ta tabbatar masa da ingancin tsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya bukaci a fara amfani da na'urar kada kuri'a a duk zabubbukan da ake gudanarwa a Najeriya.
Ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta rungumi fasaha domin kara inganta sahihanci, gaskiya da kuma ingancin tsarin gudanar da zabubbuka.

Source: Facebook
Wace shawara Sarkin Zazzau ya bayar?
Jaridar Daily Trust ta ce Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 9 ga watan Yulin 2026 a Kaduna yayin kaddamar da shirin dabarun shekaru biyar (2026–2030) na hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM).
"Har yanzu ina cikin 'yan Najeriya da suka yi amanna cewa dole Najeriya ta ci gaba. Maimakon amfani da tsarin kada kuri'a na takarda, ya kamata a rika amfani da na'urar kada kuri'a a kowane zabe da za a gudanar a Najeriya."
- Ambassada Nuhu Bamalli
Bamalli ya bayyana dalilin ba da shawarar
Sarkin, wanda tsohon kwamishinan KAD-SIECOM ne, ya ce wannan matsaya ta samo asali ne daga gogewar da ya samu bayan ziyarce-ziyarcen nazari da ya yi zuwa China, Brazil da Amurka domin koyon yadda ake amfani da tsarin kada kuri'a na na'ura.
Ya tuna cewa tawagar Kaduna ta ziyarci birnin Shenzhen na kasar China, inda aka kera na'urorin kada kuri'ar, sannan daga bisani suka halarci zabubbukan da aka gudanar da wannan fasaha a Brazil da Amurka.
Yadda Kaduna ta yi amfani da tsarin
Bamalli ya ce a lokacin da yake aiki a hukumar, jihar Kaduna ta samu nasarar amfani da na'urar kada kuri'a, inda aka kammala kada kuri'a da tattara sakamako cikin 'yan sa'o'i kadan.
Ya bayyana cewa an tsara na'urorin ne domin hana magudin zabe, yana mai cewa kuri'un da aka kada suna shiga cibiyar hukumar ta hanyar yanar gizo, yayin da wakilan jam'iyyun siyasa ke samun takardun sakamako kai tsaye a rumfunan zabe.
"Saboda haka har yanzu ina rokon SIECOM ta sake duba wannan batu. Abu ne mai girma, kuma ya kamata hukumar ta jagoranci wannan tsari."
- Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli

Source: Facebook
Shugabar KAD-SIECOM ta yi bayani
Tun da farko, shugabar KAD-SIECOM, Hajara Mohammed, ta ce shirin dabarun ba takardar manufofi kawai ba ce, Daily Post ta dauko labarin.
Ta bayyana cewa wata muhimmiyar hanya ce ta inganta tsarin gudanar da hukumar domin tabbatar da kwarewa, sahihanci da kuma dorewar amincewar jama'a.
A cewarta, shirin ya yi la'akari da tsofaffi da sababbin kalubalen da ke fuskantar gudanar da zabubbuka, ciki har da karancin fitowar masu kada kuri'a, matsalolin sufuri da kayan aiki, sauye-sauyen dokoki da kuma bukatar kara gina amincewar jama'a ga tsarin zabe.
Sarkin Zazzau ya dakatar da dagaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli, ya dakatar da wani dagaci kan abin da ya shafi rigimar gado.
Sarkin ya ce masarautar ba za ta lamunci duk wani nau’in yaudara ko cin zarafin marasa ƙarfi daga masu mulki ko jami’ansu ba.
Asali: Legit.ng

