COVID-19: Na zata ba zan rayu ba – Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa ya bayyana halin da ya shiga

COVID-19: Na zata ba zan rayu ba – Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa ya bayyana halin da ya shiga

Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr Doyin Okupe, a ranar Litinin ya bada labarin abinda ya fuskanta yayin da yake cibiyar killacewa don jinyar cutar coronavirus.

Bayan samun warakarsa, Okupe ya ce, da kyar ya sha sakamakon cutukan da yake fama dasu kafin kamuwarsa da COVID-19.

"Ni likita ne kuma a lokacin da zan tafi jinya, na san abinda nake shirin fuskanta. Na san duk wasu hadarurruka da zan fuskanta," ya bayyana yayin zantawa da gidan talabijin din Sunrise Daily.

Ya kara da cewa, "Shekaruna 68 kuma ina da hawan jini da ciwon sukari. A bayyane yake cewa ina da ciwuka tun kafin coronavirus ta kama ni."

COVID-19: Na zata ba zan rayu ba – Tsohon hadimin shugaban kasa ya bayyana halin da ya shiga

COVID-19: Na zata ba zan rayu ba – Tsohon hadimin shugaban kasa ya bayyana halin da ya shiga Hoto: Channels Television
Source: UGC

Okupe dai tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne. Ya ce har zuwa lokacin da ya tafi cibiyar killacewa, babu wata alamar cutar da ta bayyana tare dashi.

Ya ce, zazzabi ya fara kama shi amma ya samu taimakon likitoci a cibiyar kuma ya warke bayan kwanaki shida.

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasar ya yi bayanin cewa zazzabin da ya kwantar da shi ya biyo bayan tada hankalinsa da yayi.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su dauki dukkan jan kunnen da aka yi a kan cutar da matukar muhimmanci. Haka ne zai dakile yaduwar muguwar cutar.

Okupe ya kara da bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ke cibiyar killacewa duk cutar zazzabin cizon sauro ke damunsu ba korona ba. Ya shawarci gwamnati da ta dauki matakan da suka dace.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya nada Kashim Ibrahim-Imam shugaban TETFUND

A darussan da ya koya, yace, "Ina mika godiyata ga Ubangiji da ya bani lafiya. Na yafewa duk wanda ya taba yi mun laifi kuma ina son nima a yafe min.

"A gareni yanzu, bautar Ubangiji da kasa ta na saka gaba. Bani da wani buri a rayuwata."

A gefe guda, mun ji cewa babban alkalin jihar Yobe, Justis Musa Nabaruma, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a daren ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, bayan yar gajeriyar rashin lafiya a asibitin kasa da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan.

Wani daga cikin iyalan marigayin, Hussaini Nabaruma, ne ya tabbatar da hakan ga Channels Television a ranar Talata, 19 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel