Taraba: Dukkan masu korona na jihar sun warke, an sallamesu

Taraba: Dukkan masu korona na jihar sun warke, an sallamesu

Gwamnatin jihar Taraba ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon annobar Coronavirus a jihar kuma duk wanda ya kamu da cutar ya warke.

Mataimakin gwamnan jihar, Haruna Manu, a wata zantawa da manema labarai suka yi da shi, ya ce dukkan masu cutar a jihar sun warke.

Ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar cutar ta sake dawowa jihar saboda yadda ake take dokoki.

A kalamansa: "Muna farin cikin sanar da cewa babu mai cutar korona a halin yanzu a jihar mu.

"A don haka, ya kamata mu mayar da hankali wajen kiyaye dokokin kungiyar kiwon lafiya ta duniya. Don haka dole ne mutanenmu su dage wajen wanke hannaye, bin dokar nesa-nesa da juna da kuma kiyaye dokokin hana zirga-zirga.

Taraba: Dukkan masu korona na jihar sun warke, an sallamesu

Taraba: Dukkan masu korona na jihar sun warke, an sallamesu Hoto: The Eagle Online
Source: UGC

"Wannan hakki ne na kowanne dan jihar don bada gudumawa ga gwamnati wajen kariya daga annobar."

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa za su dauka matakan da suka hada da kara dakunan gwaji. Ya bayyana bude wuraren bauta da bai wa ababen hawa damar zirga-zirga daga karfe 8 na safe zuwa 9 na dare.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: Na zata ba zan rayu ba – Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa ya bayyana halin da ya shiga

Kamar yadda yace, "dokar takaita zirga-zirga na nan a ranakun Litinin, Talata, Laraba da Alhamis. Amma shige da fice a jihar ce ba a aminta da shi ba har yanzu."

A gefe guda, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, kashi 51 cikin 100 na duk adadin masu cutar korona a Najeriya sun kasance a wasu kananan hukumomi 9 kacal da ke fadin kasar.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya sanar da hakan da cewa kananan hukumomi 9 a Najeriya sun tattare kashi 51 cikin 100 na duk masu cutar korona a kasar.

Sanarwar Sakataren Gwamnatin ta zo ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai kan halin da kasar ta ke ciki game da annobar korona.

Boss Mustapha wanda ya kasance shugaban kwamitin kula da annobar korona a Najeriya, ya ce bincikensu ya gano cewa, wasu kananan hukumomi 9 a fadin Najeriya sun dauke nauyin duk wani adadi na masu cutar korona a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel