Dalibai da Malaman da Aka Sace a Oyo Sun Kubuta, an Samu Bayanai

Dalibai da Malaman da Aka Sace a Oyo Sun Kubuta, an Samu Bayanai

  • Dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire a jihar Oyo sun samu 'yanci bayan kwashe kwanaki a tsare
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya tabbatar da sakin su
  • Har yanzu ba a bayyana yadda aka samu nasarar ceto su ba domin ba a bayyana ko an biya kuɗin fansa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ibadan, jihar Oyo - Dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire da ke jihar Oyo sun shaki iskar 'yanci.

Dalibai da malaman dai sun sake samun 'yancinsu ne bayan shafe lokaci a tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

An ceto daliban da aka sace a Oyo
Dalibai da malaman da aka sace a Oyo Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin 2026, a shafin X.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za ka kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

A cikin wani saƙo da ya wallafa Onanuga ya ce jami'an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su.

"A ƙarshe, jami'an tsaronmu sun kuɓutar da dukkan ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a Orire, jihar Oyo," in ji shi."

- Bayo Onanuga

Har yanzu babu cikakken bayani

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka samu nasarar sakin daliban da aka sace ba.

Haka kuma ba a tabbatar da ko an biya kuɗin fansa ko kuma irin matakan da suka kai ga samun 'yancinsu ba.

Yadda aka kai harin a makarantu

An yi garkuwa da ɗaliban da malaman ne a ranar 15 ga Mayu, 2026, lokacin da wasu ɗauke da makamai suka kai hari kan makarantu uku a yankunan Esiele da Yawota na ƙaramar hukumar Oriire.

Makarantun sun haɗa da, Community Grammar School, Baptist Nursery and Primary School da L.A. Primary School.

Aƙalla ɗalibai 39 da malamai bakwai, ciki har da shugaban makaranta guda, aka yi garkuwa da su a lokacin harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'in tsaro har da sace mutane a Abuja

Malamai biyu sun rasa rayukansu

A yayin harin, wani malami mai suna Joel Adesiyan ya mutu yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga maharan. Wani malamin kuma, Michael Oyedokun, an sare masa kai a maboyar masu garkuwa da mutanen.

An ceto dalibai da malaman da aka sace a Oyo
Taswirar jihar Oyo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Buƙatun da masu garkuwa suka gabatar

Rahotanni sun nuna cewa kafin su amince da sakin waɗanda suka yi garkuwa da su, masu garkuwar sun gabatar da buƙatu guda huɗu.

Buƙatun sun haɗa da sakin wasu shugabannin 'yan ta'adda da ake tsare da su, biyan kuɗin fansa, ba su motocin Hilux guda biyu.

Sai dai gwamnatin jihar Oyo ta ci gaba da jaddada cewa ba za ta biya kuɗin fansa ba domin sakin kowane mutum da aka yi garkuwa da shi.

'Yan bindiga sun kashe jami'in tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a yankin Mpabe da ke birnin tarayya Abuja.

'Yan bindigan sun hallaka wani jami'in tsaro tare da yin garkuwa da wasu mutane uku ciki har da fasto yayin harin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com