Yadda Dan Takarar Gwamna Ya Kawo Ƙarshen Rikicin Shugabancin ADC a Kaduna

Yadda Dan Takarar Gwamna Ya Kawo Ƙarshen Rikicin Shugabancin ADC a Kaduna

  • Jam'iyyar adawa ta ADC reshen jihar Kaduna ta yi nasarar hade kan 'ya'yanta wuri guda yayin da babban zaben 2027 ke kara matsowa a Najeriya
  • An samu cimma matsaya ne bayan Isa Ashiru, 'dan takarar gwamna a jihar ya zauna da dukkanin bangarorin da ke adawa da juna tare da jin matsalar su
  • Bayan zaman, shugabannin sun amince da zubar da makamin, sannan an kuma fara ɗaukar matakan warware sauran shari'un da suka shafi rikicin shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar ADC, Isa Ashiru Kudan, ya sasanta rikicin cikin gida da ya daɗe yana addabar reshen jam'iyyar a jihar.

Sulhun ya biyo bayan wani zama na kusan sa'o'i uku da aka gudanar ranar Laraba 22 ga watan Yuli, 2026 a ofishin Ashiru da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

ADC ta nemi gwamnati ta fito da bayanai kan yadda aka kashe N17.5tr a NNPCL

ADC ta shawo kan matsalar shugabanci a Kaduna
Isah Ashiru Kudan'dan takarar gwamna a jihar Kaduna Hoto: Suleiman Abdullahi Dabai
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa shugabannin ɓangarori daban-daban na jam'iyyar, mambobin kwamitin gudanarwa da sauran manyan masu ruwa da tsaki sun halarci zaman.

ADC ta sasanta kan ta a Kaduna

Jaridar Vangyuard ta kawo labarin cewa daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Elder Patrick Ambut, Ben Bako, Tijjani Mustapha, Bege Katuka, mataimakin shugaban shiyyar jam'iyyar, Hafsat Baba da sauran jiga-jigan ADC a Kaduna.

Da yake magana bayan kammala taron, Patrick Ambut ya bayyana sulhun a matsayin wani babban ci gaba ga jam'iyyar, yana mai yabawa Isa Ashiru Kudan kan rawar da ya taka wajen haɗa kan mambobinta.

Ya ce dukkan ɓangarorin da suka samu sabani sun amince su haɗa kai domin ƙarfafa jam'iyyar tare da fara shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.

Ambut ya ce:

"Babban burinmu shi ne ganin ADC ta samu nasara a babban zaɓe mai zuwa, kuma yanzu batun rarrabuwar kawuna a Kaduna ya zama tarihi."

Kara karanta wannan

Ricikin bayan zaben fitar da gwan ya raba kan APC a jihar Niger

ADC ta fara shirin tunkarar zaɓen 2027

Shi ma da yake zantawa da manema labarai, Tijjani Mustapha ya bayyana taron a matsayin mai cike da fahimtar juna da kuma nasara.

Ya ce shugabannin jam'iyyar 11 da suka halarci zaman sun cimma matsaya kan muhimman batutuwa, inda ya ƙara da cewa za a fitar da cikakken sanarwar abin da aka amince da shi nan gaba

ADC ta ce an hade kai don tunkarar babban zabe mai zuwa
Tutar jam'iyyar hamayya ta ADC Hoto: ADC Coalitio 2027
Source: Twitter

A nasa ɓangaren, Ben Bako ya tabbatar da cewa rikicin shugabanci da ya raba kan jam'iyyar ya zo ƙarshe kuma ana ci gaba da ɗaukar matakan da za su warware sauran shari'un da suka taso sakamakon rikicin.

Bako ya bayyana cewa ingantaccen shugabanci yana bayyana ne idan aka iya haɗa mutane domin cimma manufa guda, yana mai cewa hakan ne Isa Ashiru ya nuna ta hanyar wannan sulhu.

Yadda Kudan ya koma ADC

A baya, mun kawo labarin yadda jam'iyyar haɗakar yan adawa, wato ADC na ci gaba da jan hankalin manyan ƴan siyasa kwanaki bayan an kaddamar da ita a babban binrin tarayya Abuja da shirin tunkarar APC.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fara saka bayanan 'yan takarar gwamna a shafin INEC

Tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin haɗaka don kawo karshen mulkin APC da ake yi wa kallon ta gaza a bangarori da dama.

Da yake tsokaci kan wannan ci gaba, ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP a 2023 ya ce zai shiga duk wata haɗaka da aka kafa don kawo ƙarshen mulkin danniya na Bola Ahmed Tinubu da ta karbi mulki a zaben da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng