Kwamandan Yan Ta’adda Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Kotu a Abuja Ta ba Shi Zabi
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa wanda ake zargin kwamandan kungiyar Ansaru ne zabi kan shari'ar da ake yi
- Abba da Mahmud Usman na fuskantar tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta'addanci, yayin da Usman ya riga ya amsa laifinsa
- DSS ta zargi wadanda ake kara da daukar nauyin ta'addanci, garkuwa da mutane, kera bama-bamai da kuma hulda da kungiyoyin ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa wanda ake zargin kwamandan kungiyar Ansaru mai alaka da Al-Qaeda zabi a shari'ar da ake yi.
Kwamandan yan ta'addan, Abubakar Abba wanda aka fi sani da Abu Bara ya samu wa'adin kwanaki 11 domin yanke shawarar ko zai sauya amsar rashin laifin da ya bayar tun farko.

Source: Facebook
An gurfanar da kwamandan yan ta'adda a kotu
Hukumar DSS na gurfanar da Abba tare da Mahmud Usman, wanda aka fi sani da Isah Adam ko Mahmud Al-Nigeri, bisa tuhume-tuhume 32 da suka shafi laifukan ta'addanci, cewar The Nation.
A lokacin gurfanarsu a farkon wannan shekara, Mahmud Usman ya amsa laifin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba domin samar da kudaden daukar nauyin ta'addanci da sayen makamai, inda kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15.
Sai dai ya musanta sauran tuhume-tuhume 31, yayin da Abubakar Abba ya musanta dukkan tuhume-tuhume 32 da ake masa.

Source: Twitter
Kwamandan yan ta'adda ya shiga waswasi
A zaman kotun, Abba ya sanar da kotun cewa yana son janye amsar rashin laifin da ya bayar a baya, amma bayan tattaunawa da lauyarsa, Husseina Tukur, ya ce har yanzu bai yanke shawarar ko zai sauya amsarsa ko zai ci gaba da rike ta ba.
Lauyan masu gabatar da kara, David Kaswe, ya yi adawa da sake dage shari'ar, yana mai cewa wanda ake kara ya taba neman irin wannan damar a zaman da ya gabata.
Ya bukaci kotun ta ci gaba da sauraron shari'ar idan har wanda ake kara ya kasa yanke shawara kan matakin da zai dauka, cewar Punch.
Da yake yanke hukunci kan bukatar, Mai Shari'a Emeka Nwite ya ce tunda Abba ne ya fara gabatar da wannan bukata a gaban kotun, ya dace a ba shi damar yanke shawara.
Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 20 ga Yuli domin Abba ya bayyana matsayinsa, sannan a ci gaba da sauraron shari'ar.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar DSS ta kama wadanda ake karar ne a wasu samame daban-daban da ta gudanar tsakanin Mayu da Yulin shekarar 2025.
Bodejo ya amincewa da zargin ta'addanci
An ji cewa shugaban Miyetti Allah a Najeriya, Bello Bodejo, ya yi magana a kotu game da tuhume-tuhume 12 da EFCC ta shigar.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Bodejo a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin da ya shafi dala miliyan 2.63.
Bayan karanta tuhume-tuhumen a kotu, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari'ar domin ci gaba da gudanar da shari'a.
Asali: Legit.ng

