Tsadar fetur: Yan Najeriya na Fuskantar Sabuwar Barazana Ta Tsadar Abinci

Tsadar fetur: Yan Najeriya na Fuskantar Sabuwar Barazana Ta Tsadar Abinci

  • Rikicin da ke ci gaba da zafi a yankin Gabas ta Tsakiya ya kara dagula farashin ɗanyen mai ya haura Dala 100 kan kowace ganga
  • Masana sun yi gargaɗin cewa farashin fetur, sufuri da kayan abinci na iya ƙara tashi a lokacin da Najeriya ke kokarin daidaita farashin fetur
  • Duk da matsin da jama'a za su iya fuskanta, an gano cewa Gwamnatin Tarayya na iya samun ƙarin kuɗaɗen shiga da ba a tanada a kasafin kuɗi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ana hasashen 'yan Najeriya za su sake fuskantar ƙarin tsadar rayuwa bayan da farashin ɗanyen mai ya haura Dala 100 kan kowace ganga.

An samu karin hauhauwar farashin fetur ne sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Amurka da Iran wanda ke kawo cikas ga jigilar man.

Kara karanta wannan

Idon Trump ya koma kan kadarorin Iran da ke Amurka, ya fara kai masu barazana

Ana tsoron farashin mai zai kara lulawa sama
Wasu yan Najeriya a gidan mai, jama'a su na harkokinsu na sufuri a titin kasar Hoto: Getty
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa farashin ɗanyen man Bonny Light na Najeriya ya zarce Dala 100 a karon farko tun watan Mayun 2026.

Dalilin tashin fetur a Najeriya

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an samu karin farashin biyo bayan fargabar cewa rikicin Gabas ta Tsakiya zai iya kawo cikas ga samar da mai a duniya.

Yankin Gabas ta Tsakiya na samar da kusan kashi ɗaya bisa uku na ɗanyen man da ake fitarwa zuwa kasuwannin duniya. Masana sun ce idan rikicin ya ci gaba, farashin mai na iya ci gaba da hauhawa.

Kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na shekarar 2026 ya dogara ne da farashin Dala 64.85 kan kowace ganga, samar da ganga miliyan 1.84 a rana da kuma musayar N1,400 kan Dala ɗaya.

Najeriya na iya samun karin kudin shiga

Da farashin da ake samu yanzu, Najeriya na samun kusan Dala 35 fiye da abin da aka tsara a kasafin kuɗi kan kowace ganga ta danyen mai.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kashe N500m a kare martabar Najeriya kan zargin gallazawa kiristoci

Sai dai hukumar NUPRC ta ce samar da mai na ƙasa yana kusan ganga miliyan 1.7 a rana, ciki har da abin da ta kira condensate, wanda zai iya rage yawan kuɗin da ake sa ran samu

Ana sa ran Najeriya za ta kara samun kudin shiga
Shugaban Najeriya a ofishinsa da ke Aso Rock Villa Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Masana tattalin arziki sun ce duk da cewa gwamnati za ta iya amfana da ƙarin kuɗaɗen shiga, jama'a za su fi jin raɗaɗin hauhawar farashin fetur saboda tsarin kasuwar man fetur da aka 'yanta.

Sun bayyana cewa idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da tashi, kuɗin shigo da fetur daga ƙasashen waje zai ƙaru, lamarin da zai sa masu kasuwanci ƙara farashin man fetur a gidajen mai.

Dangote ya dawo sayar da fetur da Naira

A baya, kun samu labarin cewa matatar Dangote ta koma sayar da fetur da Naira bayan dakatar da tsarin na ɗan lokaci tare da fara amfani da Dalar Amurka biyo bayan koarfin yan kasuwar Najeriya.

Kamfanin ya ƙara farashin man fetur daga N1,075 zuwa N1,215 kan kowace lita, wanda ya nuna ƙarin N140, hakan ya nuna karin 13%, lamarin d aya jawo koke daga yan kasuwa da mutanen gari.

Masu harkar mai sun ce sabon matakin ya kawo ƙarshen damuwar da tsarin biyan kuɗi da Dala ya haifar a kasuwar man fetur, wanda ya jawo har wasu daga cikin yan kasuwar IPMAN su ka dakatar da sayen fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng