Yadda Matar El Rufai Ta Sa Peter Kuka Ya Tausaya wa Halin da Suka Shiga

Yadda Matar El Rufai Ta Sa Peter Kuka Ya Tausaya wa Halin da Suka Shiga

  • Peter Obi ya yi kuka da ya ji kalaman da suke fitowa daga bakin Hajiya Asiya El-Rufai da ta kira taron manema labari
  • Matar tsohon gwamnan ta bukaci Bola Ahmad Tinubu ya tsoma baki domin ganin EFCC ta saki Malam Nasir El-Rufai
  • Asiya ta tuna wa Shugaban Najeriyan yadda suka taya shi kamfe, wannan ya sa Obi ya ji tausayin halin da suka shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Peter Obi, mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NDC ya yi kuka da ya ji wani jawabin Asiya El-Rufai.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya yi kwana da kwanaki a garkame, hakan ta sa Asiya El-Rufai ta fito tana rokon a saki mai gidansu.

Nasir El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai, Peter Gregory Obi, da wasu iyalin tsohon gwamnan Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai, Peter Obi, Explorer Hausa
Source: Facebook

Matan El-Rufai na so ICPC ta sake shi

The Cable ta ce wasu matan El-Rufai sun kira taron manema labarai, suna rokon Bola Ahmed Tinubu ya sa ICPC ta saki mijinsu.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga: Kungiyar duniya ta yi wuf ta yi magana da jin an cafke malami a Katsina

Asiya, mata ta biyu da ‘dan siyasan ya aura ta bukaci shugaban kasa ya sa baki a binciken da ake yi wa El-Rufai bayan ya bar ofis.

Hajiya Asiya ta ce iyalin tsohon ministan Abuja sun bukaci hakan ne domin kowa yana damar zuwa asibiti, ya ga iyalinsa ko lauya.

Kai tsaye dattijuwar ta tuna wa Mai girma Bola Tinubu rawar da mai gidanta ya taka lokacin da yake neman mulki a zaben 2023.

Peter Obi ya soki kama El-Rufai

Mista Peter Obi ya fitar da jawabi a ranar Laraba, yake cewa dole a yi adalci da gaskiya a shari’ar da El-Rufai yake yi da hukumomi.

‘Dan takaran na shugaban kasa ya ce bai kamata a yi amfani da beli a matsayin wani makami ba, ya bayyana ra'ayinsa a shafin X.

“Na farka da safiyar yau a Amurka, kuma na kadu sosai da bidiyon Hajiya Asiya El-Rufai, ya jawo na yi dogon tunani game da makomar kasarmu.
"Dole mu guje wa rashin adalci wajen shari’a wanda yake shafe amannar jama’a da gwamnati kuma ya ke barazana ga hadin kai.

Kara karanta wannan

ICPC: Jam'iyyar ADC ta jero bukata 6 da ta yi maganar mugun halin da El Rufai ke ciki

"Dole masu tabbatar da bin doka su yi aiki da kyau kuma su bi ka’ida da kyau."

- Peter Obi

Tsohon gwamnan Anambra ya yi kira a hada-kai wajen ganin an tabbatar da adalci da kare martaba, ya ce haka ake so kasar ta zama.

Obi bai Najeriya a lokacin hada rahoton, amma yana ta jefo da maganganun da ke nuna bai tare da gwamnati a kan lamarin Malam El-Rufai.

ADC: Mai karar alkalai a kotu zai biya N100m

Labarin da ya zo mana shi ne zargin alkalai da son kai a karar Nafiu Bala Gombe ya sa shugaba a ADC zai biya N100m a matsayin tara.

Tuhumar alkalai da son kai a shari'ar Nafiu Bala da David Mark ya sa sakataren jin dadin ADC zai biyan kudi saboda ya bata alkalan kotu.

Reshe ya juye da mujiya domin sakataren na jam'iyyar APC ne ya kai alkalai kara saboda zargin sun nuna son kai a shari'ar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng