‘An Fada Mani Hatsarinsa’: Gwamna kan Gargadinsa game da Takara da Tinubu
- Gwamna Seyi Makinde ya ce wani jigon APC ya taba yi masa gargadi game da takarar shugaban kasa a 2027
- Makinde ya ce washegarin gargadin ne EFCC ta nemi bayanan duk kwangiloli da biyan kuɗaɗen gwamnatin Oyo tun daga 2021
- Gwamnan ya ce kotu ta tabbatar EFCC na da ikon bincike, amma ta ce dole binciken ya kasance bisa doka, hujja da bin kundin tsarin mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya yi magana game da hatsarin da ke cikin yin takara da Bola Tinubu.
Makinde ya bayyana cewa wani jigon jam'iyyar APC ya taba gargade shi kada ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2027 bayan da jam'iyyar ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta.

Source: UGC
Makinde ya bayyana hakan ne cikin wasiƙarsa ta wata-wata ta Yulin 2026, wadda jaridar Punch ta samu a Ibadan inda ya yi karin haske kan batutuwan siyasa.
Yadda EFCC ta fara binciken Makinde
Ya ce wannan bayani ya zo ne yayin da yake mayar da martani kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan, wadda ta hana Hukumar EFCC ci gaba da binciken da ta shirya yi kan kuɗaɗen gwamnatin Oyo.
Makinde ya ce washegarin gargadin da ya samu daga jigon APC, EFCC ta aika wasiƙa tana neman kwafen duk kwangilolin gwamnatin Oyo da kuma biyan kuɗaɗen 'yan kwangila daga shekarar 2021.
Sai dai ya ce hukumar ba ta bayyana sunan wani ɗan kwangila, kamfani, wata ma'amala ko wani takamaiman laifi da take bincike a kai ba kafin neman bayanan.
Kotun ta bayyana cewa EFCC na da ikon gudanar da binciken laifukan kuɗi kamar yadda doka ta tanada, amma dole ne ta yi hakan cikin iyakar kundin tsarin mulki da bin doka.

Source: Facebook
Rokon da Makinde ya yi ga EFCC
A cewar sanarwar mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sulaimon Olarenwaju, kotun ta ce irin wannan neman bayanai ba tare da takamaiman zargi ba ya yi kama da binciken neman abin da za a samu.
Makinde ya ce gwamnatinsa ba ta hana EFCC gudanar da bincike ba, sai dai ta roƙi hukumar ta fayyace waɗanne kwangiloli ko ma'amaloli take son bincika domin a miƙa mata takardun da suka dace.
Ya ce EFCC ba ta mayar da martani ga wannan buƙata ba, lamarin da ya sa gwamnatin Oyo ta garzaya kotu domin neman fassarar doka kan sahihancin irin wannan buƙatar.
Gwamnan ya ce kotun ta bayyana cewa duk wani neman bayanai dole ne ya kasance yana da alaƙa da takamaiman zargi, ba wai bincike na bazata domin neman kuskure ba.
Makinde ya mika mulki ga mataimakinsa a Oyo
An ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta amince da hutun shekara da Gwamna Seyi Makinde zai fara daga 10 ga Agusta, 2026.
Mataimakin gwamna Bayo Lawal ne zai jagoranci harkokin gwamnatin jihar har zuwa lokacin da Makinde zai dawo daga hutun.
Yan majalisar sun bayyana kwarin gwiwar cewa ayyukan gwamnati za su ci gaba ba tare da tsaiko ba yayin da gwamnan yake hutu.
Asali: Legit.ng


