Tinubu Ya Kwantar wa ’Yan Najeriya Hankali, Ya Yi Alkawarin Romon Dimukradiyya
- Shugaba Bola Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya alkawari game da tsare-tsaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa a fadin kasar
- Tinubu ya ce gyare-gyaren tattalin arziki suna bukatar hakuri da sadaukarwa, yana mai jaddada cewa ribarsu za ta bayyana nan gaba
- Shugaban ya bukaci masu fafutukar siyasa su gina hadin kai, su saurari jama'a tare da karfafa dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za su ga tasirin sauye-sauyen gwamnatins.
Tinubu ya sha alwashin cewa tsare-tsaren za su kai ga dukkan al'ummar kasar, yana mai cewa an tsara manufofin ne domin shimfida tubalin ci gaba da wadata mai dorewa.

Source: UGC
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja wanda Godswill Akpabio ya wakilce shi a wajen taron, cewar Punch.
Dalilin tsauraran matakai da Tinubu ke dauka
Ya ce gwamnatinsa ta zabi hanyar jajircewa da daukar matakai masu wahala domin ceto Najeriya da kuma gina kyakkyawar makoma ga al'umma.
Tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023, gwamnatin Tinubu ta aiwatar da sauye-sauye da suka hada da cire tallafin man fetur da hada kasuwannin canjin kudaden kasashen waje domin farfado da tattalin arziki.
Ko da yake wadannan manufofi sun haifar da damuwa a tsakanin wasu 'yan Najeriya saboda tasirinsu na gaggawa, shugaban ya ci gaba da jaddada cewa za su samar da anfani mai dorewa a nan gaba.
A cikin sakonsa, Tinubu ya ce kowace babbar kasa tana ginuwa ne ta hanyar gudunmawar kowane dan kasa da kuma kowace al'umma, yana mai cewa dimokuradiyya mai dorewa tana bukatar gaskiya, sauraron jama'a da kuma cika alkawuran gwamnati.
Ya ce gyara ba abu ne da ake yi sau daya ba, tafiya ce mai bukatar hakuri, kuma manufarta ita ce samar da rayuwa mai inganci, karin damammaki da ci gaba ga al'ummomin da za su zo nan gaba.

Source: Twitter
Tinubu ya bukaci hadin kai daga yan Najeriya
Shugaban ya kara da cewa ci gaba mai dorewa ba ya samuwa ba tare da sadaukarwa na wani lokaci ba, saboda haka ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da ba da hadin kai.
Tinubu ya bayyana cewa bangaren zartarwa, majalisa da kuma jama'ar Najeriya suna aiki tare domin tabbatar da cewa kowane dan kasa ya amfana da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Ya kuma ce siyasa kada ta zama sanadin rabuwar kawunan al'umma, yana mai jaddada cewa Najeriya ta fi kowace jam'iyya, mukami ko sakamakon zabe muhimmanci, cewar Tribune.
Ya bukaci mambobin kungiyar PBAT Door-to-Door da aka kaddamar su kasance jakadun dimokuradiyya, su rika mutunta jama'a, sauraron ra'ayoyinsu da kuma karfafa hadin kai.
Akpabio ya yi hasashen nasarar Tinubu
Kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa jam'iyyun adawa sun shirya abin da za su fada bayan an ayyana shugaban kasa a 2027.
Akpabio ya bayyana hakan ne bayan yakininsa na cewa shugaba mai ci Bola Ahmed Tinubu ne zai koma kujerarsa bayan an kammala kada kuri'a a zaben.
Ya bayyana haka ne a wta tattaunawa da ya yi da 'yan kungiyar City Boy da suka dauko tallata Tinubu a fadin Najeriya gabanin siyasar 2027.
Asali: Legit.ng


