Bayan Sharadin Trump, Netanyahu Ya Yi Magana kan Kulla Yarjejeniya da Saudiyya
- Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shigar Saudiyya cikin yarjejeniyar Abraham zai zama babban ci gaba ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya
- Trump ya ce yarjejeniyar nukiliyar farar hula da Saudiyya ta dogara ne kan shiga yarjejeniyar Abraham da daidaita hulɗa da Isra’ila
- Riyadh ta ce ba za ta amince da Isra’ila ba har sai an samar da ingantacciyar hanyar kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tel-Aviv, Israila - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan yiwuwar daidaita alaka da kasar Saudiyya.
Benjamin Netanyahu ya ce idan Saudiyya ta shiga cikin yarjejeniyar Abraham, hakan zai zama “babban tarihi wajen samun ci gaba ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya”.

Source: Getty Images
Netanyahu ya bayyana hakan ne a cikin wata gajeruwar sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026 a shafin X.
Me Netanyahu ya ce kan yarjejeniyar?
Netanyahu ya ce haɗin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila wajen kai hari kan gwamnatin Iran da kuma murƙushe ƙungiyoyin ta’addanci da ke da alaƙa da Iran ya samar da damar faɗaɗa da’irar zaman lafiya.
Ya rubuta cewa:
“Kamar yadda Shugaba Trump ya ce, shigar Saudiyya cikin yarjejeniyar Abraham zai zama babban tarihi wajen samun ci gaba ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Zaman lafiya ta hanyar ƙarfi.”
A farkon yau, Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar nukiliyar da gwamnatinsa ta rattaba hannu da Saudiyya a wannan makon tana da wani sharadi, wato Saudiyya ta shiga yarjejeniyar Abraham tare da daidaita hulɗarta da Isra’ila.
Ya ce yarjejeniyar nukiliyar farar hula da Ma’aikatar Makamashi ta Amurka ke kulla wa da Saudiyya, wadda za ta kasance ne domin amfanin farar hula ba na soja ba, za a amince da ita ne kawai idan Saudiyya ta shiga cikin yarjejeniyar Abraham.
Trump ya ƙara da cewa Amurka ba ta adawa da cibiyoyin nukiliya na farar hula da ba sa amfani da makamashin nukiliya da aka inganta.
Amurka za ta taimakawa Saudiyya
A daren jiya, Amurka ta sanar a hukumance cewa ta rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da Saudiyya, wadda za ta bai wa Riyadh cikakken taimako wajen haɓaka shirin nukiliya domin amfanin farar hula.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki na tsawon shekaru 30, kuma za ta bai wa kamfanonin Amurka damar ba da rance da kuma gina tashoshin samar lantarki na nukiliya a Saudiyya.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, an kuma tsara wata hanya ta sanya ido wadda za ta yi aiki kai tsaye da gwamnatin Amurka, ba tare da aiki tare da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ba.

Source: Getty Images
Riyadh ba ta tanka ba
Har zuwa yanzu, mahukunta a Riyadh ba su mayar da martani a bainar jama’a kan kalaman Trump ba.
Sai dai Saudiyya ta sha nanata cewa ba za ta amince da Isra’ila ba har sai an samar da ingantacciyar hanyar kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta.
Trump bai bayyana cewa yarjejeniyar ta dogara ne kan Saudiyya ta shiga yarjejeniyar Abraham ba lokacin da aka sanar da ita a ranar Laraba.
A halin yanzu, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain, Sudan, Morocco da Kazakhstan ne ke cikin ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Abraham.
Batun cafke Netanyahu a Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba za a kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ba idan ya kai ziyara ƙasar Amurka.
Shugaba Donald Trump ya bayyana ya jaddada cewa babu wani yanayi da zai sa a cafke Netanyahu yayin da yake a kasar Amurka.
Asali: Legit.ng


