Hadimin Tinubu Ya Bayyana yadda Rayuwar Najeriya Ta Fi Ta Birtaniya Sauki

Hadimin Tinubu Ya Bayyana yadda Rayuwar Najeriya Ta Fi Ta Birtaniya Sauki

  • Daniel Bwala ya bayyana bambancin rayuwa tsakanin 'yan Najeriya da ke rayuwa a Birtaniya da wadanda suke gida
  • Ya ce tsadar rayuwa, haya da sauran kudade na rage yawan abin da ma'aikata ke ragewa, lamarin da ke sa wasu yin ayyuka biyu ko uku
  • Bwala ya ce gwamnatin Tinubu ta bullo da tallafin lafiya, ciki har da rangwamen kashi 50 na dialysis da tiyatar haihuwa kyauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya yi magana kan bambancin rayuwa a Najeriya da Birtaniya.

Bwala ya ce wasu 'yan Najeriya da ke aiki a Birtaniya kuma suke samun tsakanin fam £2,600 zuwa £2,800 a wata na iya kasancewa cikin mawuyacin hali fiye da mutumin da ke samun albashin N60,000 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Al Jazeera ta ba hadimin Tinubu hakuri a asirce kan wata hira da suka yi

Bwala ya fadi bambancin rayuwar Najeriya da Birtaniya
Hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu, Daniel Bwala yayin hira da yan jarida. Hoto: Bwala Daniel.
Source: Twitter

Bwala ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Morayo Afolabi Brown Show da aka wallafa a YouTube.

Bwala ya magantu kan tsadar rayuwa a Najeriya

Daniel Bwala ya yi bayani kan yadda tsadar rayuwa ke shafar ma'aikatan Najeriya da ke zaune a Birtaniya.

Ya ce daga cikin kudin shigar da suke samu, ana kashe mafi yawansa wajen biyan kudin lantarki, intanet, talabijin da haya, inda ya ce kudin haya kadai na iya kaiwa kusan fam 800.

Bayan biyan wadannan kudade da kuma ciyar da kai, Bwala ya ce abin da ke ragewa ba ya da yawa, wanda ke tilasta wa wasu yin ayyuka biyu ko uku domin su iya rayuwa.

Da yake kwatanta hakan da mai albashin naira 60,000 a Najeriya, Bwala ya ce duk da karancin kudin shiga, irin wannan mutum na iya samun taimako daga dangi da abokai lokacin da yake cikin bukata.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

Sai dai ya amince cewa matsalar mai albashin N60,000 ita ce rashin isasshen kudi domin gina gida ko sayen mota, amma ya ce hakan ba yana nufin rayuwar ma'aikatan Birtaniya ta fi sauki ba.

Bwala ya bayyana cewa mutanen da suka yi hijira zuwa Birtaniya, har da masu digirin farko da na biyu, galibi suna karewa ne da aikin kula da tsofaffi da marasa lafiya, wanda ya kwatanta da wani nau'in bautar zamani.

Ya ce ya san mutane masu digirin digirgir da na biyu da ke aiki a rumbunan ajiya tare da sauran ma'aikata karkashin shugabannin da ba su da ilimin sakandare.

Bwala ya yabawa gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da hadiminsa, Daniel Bwala a fadar shugaban kasa. Hoto: Bwala Daniel.
Source: Twitter

Yabon da Bwala ya yi ga Tinubu

Da yake mayar da martani ga tambayar da aka yi masa kan yawan masu neman biza saboda talauci, rashin tsaro da rashin aikin yi, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da manufofin rage wa jama'a wahalhalu.

Ya ce gwamnati ta samar da rangwamen kashi 50 cikin 100 na kudin dialysis a asibitocin tarayya tare da samar da tiyatar haihuwa ta hanyar 'Caesarean' kyauta.

Sai dai ya ce har yanzu gwamnati ba ta da isassun kudade da za ta fadada irin wadannan tallafi zuwa asibitoci masu zaman kansu da kuma wasu magunguna.

Kara karanta wannan

Da gaske alkalin da ya ba Tinubu nasara a kotu a zaben 2023 ya makance?

'Al Jazeera ta ba shi hakuri a asirce' - Bwala

An ji cewa Hadimin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da titsiye da wani babban ɗan jarida ya yi masa.

Daniel Bwala ya ce kafar Al Jazeera ta ba shi hakuri a asirce kan hirarsa da Mehdi Hasan, amma ta ki fitarwa a bainar jama'a.

Bwala ya ce an gyara hirar ta hanyar cire wasu muhimman sassa da suka nuna yana kalubalantar Hasan, lamarin da ya kira rashin da'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.