Rikici kan Tace Fim: Abin da Ya Sa Gwamnati Ke Hana Nuna Wasu Fina Finan Kannywood

Rikici kan Tace Fim: Abin da Ya Sa Gwamnati Ke Hana Nuna Wasu Fina Finan Kannywood

Kano - Kannywood, masana'antar fina-finan Hausa dake Arewacin Najeriya, na fuskantar matsin lamba daga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wannan hukumar na da ikon hana haska fina-finai da shirye-shirye da take ganin sun saba wa tarbiyya da tsarin rayuwar Musulunci.

Rahoto: Yadda gwamnati ke haramta haska fina-finan Kannywood da abin da ke biyo baya
Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da wasu fina-finai 22 a cikin Mayun 2025. Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

Wannan rahoto ya duba lokutan da hukumar ta haramta haska fina-finai, yadda jama’a suka dauki lamarin, da wasu muhimman abubuwan da suka biyo baya.

Dalilin hukumar na haramta wasu fina-finai

Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano, karkashi Abba El-Mustapha, ta haramta duk wasu fina-finai da suke:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Bayyana tashin gankali:

A watan Afrilu 2024, hukumar ta haramta nuna tashin hankali a fina-finai, tana danganta hakan da karuwar laifukan daba a Kano, inji rahoton BBC.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya ce fina-finai na kara haddasa dabi’un tashin hankali ga masu kallo, wanda ke hana zaman lafiya a jihar.

  • Bayyana abubuwan rashin tarbiyya:

Fina-finai da ke tabo batutuwan da ake ganin masu sosa rai ne kamar ilimin jima’i ko dabi’un da ake kira marasa da’a, su kan fuskanci takunkumi.

Misali, an dora fim din Makaranta na 2022 da ya tabo ilimin jima’i da matsalar kaciya, bisa ma'auni na rashin tarbiyya.

  • Ayyukan 'yan daudau

Mun ruwaito cewa, hukumar ta haramta duk wani fim da ke dauke da mutum mai sanya kaya na wani jinsi daban da na sa (daudu), tana mai cewa hakan ya sabawa al’adun yankin.

Wannan yunkuri yana daga cikin kokarin tabbatar da bin dokokin Shari’a a Kano, daya daga cikin jihohi 12 da ke aiwatar da dokar Musulunci.

  • Karya dokokin tantancewa:

A watan Mayun 2025, muka ruwaito cewa hukumar ta dakatar da wasy fina-finai 22 ciki har da Labarina da Dadin Kowa saboda rashin gabatar da su domin tantancewa kafin a sake su.

Hukumar ta bukaci a dakatar da watsa fina-finan har sai ta amince da su, tare da gargadin hukunci ga wadanda suka karya doka.

Wannan dakatarwa ta jawo ce-ce-ku-ce mai zafi, musamman daga daraktoci da masu shirya wadannan fina-finan, ciki har da Haruna Talle Mai Fata.

Wadannan matakai na hukumar na nuna kokarinta wajen tabbatar da fina-finai masu dauke da "kyawawan darussa" da suka dace da al’adar Kano.

Ra'ayin jama'a kan matakan hukumar tace fina-finan

Masu goyon bayan matakin:

Wasu mazauna Kano da malamai na marawa matakin hukumar baya, suna kallon hakan a matsayin kariya ga dabi’u da imanin al’umma.

Hukumar ta bayyana cewa korafe-korafen jama’a da shawarwarin malamai (ulama) ne ke taimakawa wajen daukar ire-iren wadannan matakai.

Misali, a Janairun 2025, mun ruwaito cewa an dakatar da saurarorin wakokin Soja Boy da shi kansa mawakin da wasu jarumai mata biyu bayan bullar wasu bidiyon mawakin da ke nuna fitsara.

A zantawarmu da Alaramma Tanimu Mai Sittin, a jihar Kano, ya ce barin mutane irinsu Soja Boy suna yada alfasha zai iya jawo fushin Allah a kan jama'a.

"Ba na kallon kowane shiri, ko a gidana, idan ba tashoshi na addini ba, ba sa kallo, a baya ni ban ma yarda da sanya talabijin a gidan ba, amma wasu dalilai suka sanya na amince.
"Na fara cin karo da abubuwan da suka shafi shi wannan mawakin soja boy, na yi mamaki da gwamnati ba ta taka masa burki ba, amma sai na gano ashe ba mazaunin Kano ba ne.
"To koma a ina yake, barin irinsa suna yada alfasha, babbar masifa ce ga jama'a. Abin da muke tsoron yaranmu su dauka daga turawa, shi yanzu ya kawo mana har gida. To mu kuka da fushin Allah a kan mu."

Masu adawa da matakin gwamnati:

Wasu masu shirya fina-finai da al’umma na ganin cewa wadannan matakan da hukumar tace fina-finai ke dauka na tauye ’yancin fasaha.

Darakta Aminu Mukhtar Umar, wanda aka haramta masa fim din Makaranta, ya soki tsarin hukumar, yana mai shawartar a yi hadin gwiwa da masana wajen gyara fina-finai maimakon sanya masu takunkumi.

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa (CITAD) ta soki dakatarwar 2025 ta fina-finai 22, tana ganin hakan cin zarafin ’yancin jama’a ne, inji rahoton Tribune.

Wakiliyar Legit Hausa, A'isha Ahmad ta zanta da Haruna Talle Mai Fata game da wannan dakatarwa da aka yi, ciki har da fim dinsa mai suna Tawakkaltu.

Haruna Mai Fata ya ce ko kadan, hukumar tace fina-finan ba ta yi amfani da kwarewa wajen dakatar da fina-finai, musamman fim dinsa, yana mai cewa:

"An kira ni an ce an dakatar da Tawakkaltu, sai abin ya ba ni dariya. Hukumar da ta dakatar da fina-finan ta Kano ce, ni kuma ina Jos, to me ya hada fim dina da hukumar?
"Ni dan Jos ne, a Jos na dauki fim dina, ban ga dalilin da zai sa abin da aka yi a Jos ya danganci Kano ba. Kuma ni fim dina a YouToube na sake shi, ban je Kano na sake shi ba.

"Idan mutum 100 ne a cikin fim din, to jarumai 'yan Kano ba su fi mutum biyu ba, Malam Inuwa da Tahir Fagge, to menene hadin fim din da Kano shi ne ban sani ba."

Fina-finan da aka taba dakatarwa

  • Fatwa kan Saliha? (1999):

Fim din Saliha?, wanda ya nuna wata yarinya mai yawan sanya hijabi ta na aikata zina, ya jawo wata kungiyar addini a Kaduna ta bayar da fatwar kashe darakta da mai shirya fim din.

Ƙungiyar ta bukaci a janye fim ɗin daga kasuwa tare da neman gafara daga al’ummar Musulmi daga masu shirya fim ɗin.

Wannan al’amari ya nuna yadda fina-finan Kannywood ke haduwa da zafin ra’ayin addini a Arewacin Najeriya a cewar makalar da Alice Evans ta wallafa a ranar 18 ga Oktobar 2024 a shafin The Great Gender Divergence, mai taken: Fadi tashin fina-finai a karni na 20

  • Haramta fim din Makaranta (2022):

Fim din Aminu Mukhtar Umar na Makaranta ya fuskanci takunkumi saboda tabo ilimin jima’i da matsalar kaciya, inda har aka nemi jarumin ruwa a jallo.

Hukumar tace fina-finai da dab'in ta bayyana fim din Makaranta a matsayin tsantsar rashin tarbiyya, wanda ya nuna matsayinta kan sabawa al’ada.

Daraktan fim din, Aminu ya shaida wa BBC Pidgin cewa bai yi fim ɗin domin Kano ko mutanen Hausawa kaɗai ba, kuma bai ga dalilin da yasa hukumar tace fina-finai za ta tsoma baki a harkokinsa ba.

“Da na ji cewa hukumar tace fina-finai ta Kano na nemana, ban firgita ba ko kaɗan, domin nasan ban yi wani abu da ya sabawa doka ba," inji Aminu Mukhtar.
Masana'antar Kannywood na fuskantar matsin lamba daga hukumar tace fina-finai ta Kano
Wasu daga cikin jaruman Kannywood a wani taro da kamfanin NNPCL ya shirya a Abuja. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Naziri kan tukunkumin da ake sanya wa fina-finai

Matakan hukumar tace fina-finai ta Kano na nuna alaka da tarihin dokar tace fina-finai a duniya, inda hukumomi ke kokarin daidaita labarai da ra’ayoyin al’umma ko na siyasa.

A Kano, dokar Shari’a na kara karfafa wannan iko, inda ake fifita daidaito da al’ada fiye da ’yancin fasaha.

Amma irin wannan tsari yana haifar da tambayoyi: Shin hakan adalci ne? Shin yana hana ci gaban masana’antar da ke yada al’adun Hausa da samar da dubban ayyuka?

A tarihin Amurka, irin wannan tsari ya faru da dokar Hays Code (1930–1966), wadda ke iyakance abun da za a nuna a fina-finai.

Daga baya kotuna Amurka ta bayyana hakan a matsayin sabawa First Amendment, wato ’yancin fadar albarkacin baki.

Amma Kano na aiki ne da wata doka da al’ada daban, inda Shari’a da ra’ayin jama’a ke da matukar tasiri kan matakan da hukumar tace fina-finan ke dauka.

Kammalawa

Matakan da hukumar tantance fina-finai ta Kano ke dauka kan Kannywood na nufin kare darajar Musulunci da magance matsalolin zamantakewa kamar tashin hankali da rashin da’a.

Yayin da wasu ke ganin hakan ya dace da kare al’ada, wasu, musamman masana’antar fina-finai da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, na kallon hakan a matsayin danniya ko mugun amfani da iko na siyasa.

Yayin da masana’antar ke ci gaba da fuskantar kalubale, muhawarar kan tace fina-finai a Kano na nuna yaki tsakanin adana al’ada da samar da ’yancin fadin albarkacin baki.

Kannywood: Matsalar da jarumai mata ke fuskanta

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yar wasan Kannywood, Hafsat Tuge, ta yi magana kan kallon da ake yi wa 'yan fim mata a matsayin wadanda ba su dace da aure ba.

Wacce aka fi sani da Amaryar TikTok, ta ce 'yan matan Kannywood suna zaman aure kuma suna girmama mazajensu, akasin tunanin mutane.

Amma da aka tambaye ta lokacin da za ta yi aure, Hafsat ta bayyana cewa aure yana da lokacinsa, amma a ba shi ne a gabanta yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.