An ba Atiku Abubakar Mafita kan Wanda Ya Kamata Ya Zama Mataimakinsa a Zaben 2027

An ba Atiku Abubakar Mafita kan Wanda Ya Kamata Ya Zama Mataimakinsa a Zaben 2027

  • Jigon jam'iyyar adawa ta ADC, Eze Chukwuemeka Eze, ya bukaci Atiku Abubakar ya zabi Rotimi Amaechi a matsayin mataimakinsa a zaben 2027
  • Ya ce kwarewar tsohon ministan sufuri a siyasa da rawar da ya taka a zabukan baya sun sa ya dace da mukamin
  • Eze ya gargadi cewa kin zabar Amaechi na iya janyo matsala ga hadin kan jam'iyyar ADC kafin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani jigo a jam'iyyar ADC, Eze Chukwuemeka Eze, ya kawo shawara kan wanda ya dace ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027.

Eze ya bukaci dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya dauki tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin mataimakinsa a zaben shekarar 2027.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a taron kaddamar da hadakar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A rahoton da Vanguard ta tattaro, Eze ya bayyana cewa Amaechi na da dimbin gogewa a harkokin siyasa kuma ya taka muhimmiyar rawa a wasu muhimman zabukan da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Atiku da Peter Obi su sake bude wa Tinubu kofa, APC na iya lashe zaben 2027'

Dalilin da ya sa Amaechi ya dace

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Eze ya ce yadda Amaechi ya jagoranci yakin neman zaben da ya kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015 ya nuna cewa mutum ne mai tasiri da ya kamata a jawo shi a jiki.

Ya ce:

"Kana bukatar Amaechi a yanzu saboda yadda ya jagoran kamfen din da ya kayar da shugaban kasa mai ci ya tabbatar da cewa shi mutum ne da duk mai neman shugabancin Najeriya ba zai yi watsi da shi ba."

Eze ya kara da cewa Amaechi yana da karfin siyasa, tsari da kuma magoya baya da za su iya taimakawa wajen karfafa damar ADC a babban zaben 2027.

Jigon ADC ya gargadi Atiku

Jigon na ADC ya bayyana cewa duk da cewa akwai wasu sunaye da ake gabatarwa domin mukamin mataimakin shugaban kasa, ya yi imanin cewa Amaechi ne ya fi dacewa.

Ya gargadi cewa rashin zabar tsohon gwamnan Rivers din na iya haifar da matsaloli ga manufar da jam'iyyar ke son cimmawa.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

"Na ga wasu shawarwari da ake gabatar maka. Duk da cewa suna da kyau, dole ne in bayyana cewa idan ba a zabi Amaechi ba, hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga burinmu na bai daya."
Amaechi.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi yayin da magoya baya suka tarbe shi a Fatakwal Hoto: Rotimi Amaechi
Source: Facebook

Mista Eze ya yaba da kokarin Atiku

Haka kuma ya ce hakan na iya sa wasu magoya baya da mambobin ADC su ji ba a yi musu adalci ba, kamar yadda The Nation ta kawo.

Eze ya kuma yaba wa Atiku bisa kokarinsa na hada kan jam'iyyar bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Ya ce ziyarar da Atiku ya kai wa Rotimi Amaechi da Hayatu-Deen, wadanda suka fafata da shi wajen neman tikitin ADC, ta nuna cewa yana da halin hada kai da sauran shugabanni.

Me Atiku ya tattauna da Amaechi?

An ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana abin da suka tattauna da Rotimi Amaechi bayan ganawarsu a Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki musamman matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

Ya ce duk da yanayin zumunci da annashuwar da aka yi yayin ganawar, sun yi magana mai zurfi da gaskiya kan tabarbarewar da ake gani a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262